Hotunan zubar dusar kankara a Paris

Birnin Paris ya fuskanci zubar dusar kankara ta lokacin sanyi karon farko a bana, lamarin da ya kai ga fuskantar matsaloli game da harkokin sufuri, ko da yake hakan ya sa birnin ya yi kyau a wasu bangarori.

Paris ya fuskanci zubar dusar kankara karon farko a bana, inda dusar ta rufe cocin Sacré Coeur Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paris ya fuskanci zubar dusar kankara karon farko a bana, inda dusar ta rufe cocin Sacré Coeur
An rufe Eiffel Tower kusan daukacin rana domin bai wa ma'aikata damar kawar da dusar kankarar. Yanzu dai an sake bude ta domin masu yawon bude ido su je wurin. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An rufe Eiffel Tower kusan daukacin rana domin bai wa ma'aikata damar kawar da dusar kankarar. Yanzu dai an sake bude ta domin masu yawon bude ido su je wurin.
Tsawon dusar kankarar ya kai santimita 5 a babbar birnin na Faransa, lamarimn da ya sa aka fuskanci tsaiko a tasoshin jiragen kasa da na motoci. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsawon dusar kankarar ya kai santimita 5 a babbar birnin na Faransa, lamarimn da ya sa aka fuskanci tsaiko a tasoshin jiragen kasa da na motoci.
Mazauna birnin na Paris sun fito waje domin shakatawa inda aka ga wasu daga cikinsu a lambum Tuileries Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mazauna birnin na Paris sun fito waje domin shakatawa inda aka ga wasu daga cikinsu a lambum Tuileries
Mai tallan kayan kawa Masami ta baza hajarta a cikin kankara a bikin kayan kawa na lokacin sanyi na shekarar 2019 da aka yi a Grand Palais Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai tallan kayan kawa Masami ta baza hajarta a cikin kankara a bikin kayan kawa na lokacin sanyi na shekarar 2019 da aka yi a Grand Palais
Zubar dusar kankarar bai hana wadannan sabbin ma'auratan tsayawa domin a dauke su hoto ba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zubar dusar kankarar bai hana wadannan sabbin ma'auratan tsayawa domin a dauke su hoto ba
Ana sa ran dusar kankarar za ta ci gaba da sauka zuwa wasu kwanaki da ke tafe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sa ran dusar kankarar za ta ci gaba da sauka zuwa wasu kwanaki da ke tafe

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.

Labarai masu alaka

Karin bayani