Kun san abin da ya hana sanatocin Najeriya zaman majalisa?

majalisa dattawan najeriya Hakkin mallakar hoto NIGERIAN SENATE

Bisa ga dukkan alamu a Najeriya harkokin yakin neman zabe sun fara hana majalisar dokokin kasar zama yadda ya kamata.

A ranar Talata rashin halartar isassun wadanda za su yi zama ya sanya ala tilas majalisar dattijan kasar ta dage zamanta.

Hakan ya faru ne saboda rashin halartar adadin `yan majalisar da doka ta amince da shi kafin majalisar ta yi zama.

Yanzu haka dai akwai muhimman kudurori a gaban majalisar, wadanda ake jira wakilanta su yi zama domin dubawa.

Daga cikin irin wadannan muhimman abubuwa har da kudurin kasafin kudin shekara ta 2019, wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar.

A tattaunawarsa da BBC, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan, Sanata Ali Ndume ya ce duk da cewa al'amuran siyasa sun dauke hankalin wasu daga cikin wakilan majalisar to amma rashin tsari a shugabancin majalisar shi ne babban dalili.

A cewarsa "Kodayaushe idan shekaru hudu sun zo, lokacin zabe, kowa ya na zuwa fafutikar zabe, wadanda kuma ba su samu tikitin dawowa ba su na shirye-shiryen yadda za su yi da rayuwarsu.'

Ya kara da cewa shugabanci ma na daga cikin dalilan ke sa ana samun karancin sanatocin da ke zama a majalisar.

"Shugabancinmu a karkashin (Sanata Bukola) Saraki, yadda yake tafiyar da majalisar dattawa, da yawa daga ciki sun gane cewa kamar ma shirme ne, shi ya sa ba sa zuwa."

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN SENATE