An kama masu shirin kai wa Musulmai hari a Amurka

Vincent Vetromile, Brian Colaneri and Andrew Crysel Hakkin mallakar hoto Greece Police Dept
Image caption Sunayen mutane hudun Andrew Crysel mai shekara 18, da Vincent Vetromile mai shekara 19, da kuma Brian Colaneri mai shekara 20.

An kama wasu mutum uku da wani yaro daya da ake tuhumarsu da hada baki don kai hari kan wata al'ummar Musulmai a jihar New York.

Ana zargin mutanen ne da hada bama-bamai da bindigigogi da kuma shirin kai hari kan al'ummar Islamberg, wadda wani malami dan kasar Pakistan ya kirkira a shekarun 1980.

An gano shirin kai harin ne bayan da a wata makaranta wani dalibi ya jiyo tattaunawar da wasu dalibai 'yan uwansa ke yi na kitsa kai harin.

Al'ummar Islamberg ta zamo wani waje da ake yawan zargin ta zama kamar sansanin horar da masu tsattsauran ra'ayi.

Za a gurfanar da mutanen a gaban kotu ranar Laraba.

Sunayen mutane hudun Andrew Crysel mai shekara 18, da Vincent Vetromile mai shekara 19, da kuma Brian Colaneri mai shekara 20.

Dukkansu ana tuhumarsu da laifin mallakar makamai da shirya kai hari. Ana kuma tuhumar daya yaron mai shekara 16.

'Yan sanda sun ce a kalla uku daga cikinsu sun yi aiki a matsayin 'ya sikawut.

Masu bincike sun ce, kungiyar wacce take Birnin Greece da ke arewa maso yammacin jihar, ta samar da a kalla abubuwan fashewa ta hanyar amfani da manyan jarkoki da tulunan gas da allurai da sauran muggan abubuwa.

An same su a gidansu yaro mai shekara 16 din, a cewar 'yan sanda. An kuma samu bindigogi 23 a wasu wuraren daban-daban.

Al'ummar Islamberg na zaune ne a yammacin tsaunukan Catskill kuds fs Birnin Binghamton.

Mafi yawan Amurkawa 'yan asalin Afirka suna zaune ne a wannan yanki don gujewa cunkoson da ke Birnin New York.

Mazauna yankin sun bayyana al'ummar a matsayin mai son zaman lafiya da kywaun mu'amala, sai dai wasu kafafen yada labarai na bayyana su da cewa sansanin hirar da masu tsattsauran addinin musulunci ne.

Labarai masu alaka