Saudiyya za ta gayyaci Jay Z da David Beckham a 2019

An fara wallafa labarin ranar 24 ga watan Janairun 2019

yarima Muhammad Hakkin mallakar hoto Getty Images

Saudiyya ta bayyana shirye-shiryen da ta ke yi na bunkasa bangaren nishadi a kasar, wanda ya hada da bai wa gidajen abinci takardar izinin gudanar da nishadi kai tsaye, kamar yadda ake yi a kasashen Turai.

Shirin da za a kaddamar a 2019 zai kunshi shigo da taurari kamar su Jay Z da David Beckham.

Saudiyyar ta bayyana shirye-shiryen ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kisan gillar dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

Kokarin da ake yi na mayar da Saudiyya wani yankin nishadantarwa na daya daga cikin abubuwan da Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman ke yi, wanda lamarin kisan Jamal khashogji ya mutukar bata wa suna.

Waiwaye

Ko a watan Fabrairun 2018 ma Saudiyya ta ce za ta ware kudi dala biliyan 64 domin bunkasa masana'antunta na nishadantarwa a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban hukumar da ke kula da harakokn nishadi a kasar ya ce an tsara shirya abubuwa kimanin 5,000 a bana kawai, da suka kunshi har bikin cashewa na Maroon 5 kamar irin wanda ake gudanarwa a Amurka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun tuni Saudiyya ta sanar da bayar da damar bude gidajen nuna fina-finai

Akwai kuma bikin casu na Cirque du Soleil irin wanda ake gudanarwa a kasashen Turai.

Tuni dai Saudiyya ta fara aikin gina wajen casu a birnin Riyadh.

Shirin zuba jarin na cikin sabbin manufofin bunkasa tattalin arziki da ake kira Vision 2030 wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya kaddamar shekaru kusan uku da suka gabata.

Karin Labaran da za ku so ku karanta

Labarai masu alaka