Za a rataye wanda ya kashe makwabcinsa saboda janereto

Marigayin ya fadawa Tijani ya sauya mazaunin janareton na sa yanda hayaki zai daina shiga dakinsa, bayan haka ne fada ya kaure tsakinin su. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marigayin ya fadawa Tijani ya sauya mazaunin janareton na sa yanda hayaki zai daina shiga dakinsa, bayan haka ne fada ya kaure tsakinin su.

Wata kotu a Legas dake kudancin Najeriya ta yanke wa Ibrahim Tijjani dan shekara 31 hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samunsa da laifin kashe makwabcinsa.

Ibrahim dai ya kashe makwabcin nasa ne a yayin da suke fada saboda hayakin janareto.

Alkali mai shari'a Akintoye ya samu Tijjani da laifin da ake zarginsa da shi, bayan haka ne ya yanke masa hukuncin kisa.

A ranar 21 ga watan Janairun 2016 ne jaridar Vanguard a kasar ta ruwaito cewa jihar Legas ta shigar da karar gaban kotu inda Ibrahim Tijani ya musanta zargin da ake yi masa.

Adeniji kazeem wanda shi ne lauyan dake karar Tijani, ya shaida wa kotu cewa Tijani ya kashe Bashorun Okanlawon bayan ya sare shi da adda da misalin karfe 2:30 na dare a ranar 8 ga watan Fabrairun 2015.

Alkalin dai ya ce laifin dai ya saba wa dokar Najeriya karkashin sashe na 221 na kundin hukunta manyan laifuka na Jihar Legas.

Adeola Okanlawon wanda da ne ga marigayin ya shaida wa kotu cewa Tijani ya kashe mahaifinsa ne bayan mahaifinsa ya yi wa Tijani korafi a kan cewa hayakin janareto na damunsa.

Adeola ya kara da cewa mahaifin nasa ya fada wa Tijani cewa ya sauya mazaunin janareton nasa yadda hayaki zai daina shiga dakinsa, bayan haka ne fada ya kaure tsakaninsu..

Labarai masu alaka