An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

An gano sinadarai masu guba a Nafkin din yara Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar lafiya ta kasar Faransa Anes, ta ce ta gano wasu sinadari a nafkin din da ake sa wa yara wadanda za su iya cutar da yara kamar sinadarin glyphosate.

Wasu gwaje-gwaje da hukumar ta gudanar sun gano wasu sinadari wadanda ke da matukar hadari ga lafiyar dan Adam.

Hukumar Lafiyar ta ce, wannan shi ne karon farko da ta gudanar da gwaji a kan irin wadannan abubuwa.

Daga nan hukumar, ta yi kira da a dauki kwakkwaran mataki na dakile yaduwar irin wadannan nafkin din wadanda ba a kasar kadai ake amfani da su ba.

Hukumar ta ce, amfani da irin wadannan nafkin din, zai cutar da yara musamman jarirai da ya ke su aka fi yi wa amfani da su.

Ministan lafiyar kasar ta Faransa Agn├Ęs Buzyn, ya ce ana daukar kwakkwaran mataki wajen hana sayar da irin wadannan nafkin din, sai dai ya ce ba duka nafkin din ne ke da sinadarin gubar ba.

A don haka inji ministan, ba bu laifi iyaye su ci gaba da sanya wa yaransu nafkin din, amma a rinka kula sosai da irin nafkin din.

Ministan ya ci gaba da cewa, shi da takwaransa na ma'aikatar kudi da na muhalli, sun sanya hannu a cikin wata sanarwa inda suka ba wa kamfanonin da ke sarrafa irin wadannan nafkin din kwana 15 su dauki kwakkwaran mataki na dakatar da samar da irin wadannan nafkin din.

Rahoton da hukumar lafiyar kasar ta fitar, bai bayyana sunan kamfanin da ke samar da irin nafkin din ba.

Me ya sa ake ce-ce-ku-ce kan sinadarin glyphosate?

Shi ne sinadarin da ake cinikayyarsa da sunan Roundup a Amurka, akasari ana amfani da shi ne, ko da yake masu fafutukar inganta muhalli da lafiya na yawan suka a kan haka, bayan wani binciken, Hukumar Lafiya ta Duniya ya ayyana shi a matsayin "wanda zai iya janyo cutar kansa".

Nan da shekarar 2021 ne, Faransa za ta haramta amfani da sinadarin kashe ciyayin, kuma samun burbushinsa a cikin nafkin din yara, ya haifar da ka-ce-na-ce a kasar lokacin da aka fitar da rahoton.

Yanzu haka dai an bukaci manajojin kamfanonin da ke samar da nafkin din yara da su ba wa mahukunta hadin kai domin magance samar da irin wadannan nafkin din wadanda ke da illa ga lafiyar yara.

Labarai masu alaka