Jaruman Bollywood 5 da suka sadaukar da kudinsu

Shahrukh Khan da Salman Khan Hakkin mallakar hoto Getty Images

A cikin kowacce al'umma ana samun mutanen da sukan sadaukar da wani abu ga marassa galihu ko wasu masu dauke da wata lalura da dai sauransu.

A bangaren jaruman Indiya na Bollywood ma, akwai irin wadannan mutanen, wadanda ba sa damuwa da abin da suke samu wajen sadaukar da shi ga mabukata.

Wasu daga cikin irin wadannan jarumai ma suna da kungiyoyin agaji na kashin kansu baya ga taimakon da suke yi a gefe guda.

Ga biyar daga cikin jaruman Bollywood din da ke sadaukar da kudinsu ga mabukata.

Shah Rukh Khan

Hakkin mallakar hoto Variety

Shah Rukh Khan na daga cikin jaruman Bollywood da suke taimakawa marassa galihu ko kuma masu wata lalura.

Kudin da wata tawagarsa ta samu a wata gasa da aka yi bayan ta lashe gasar da suka kai 15 Crore na kudin kasar Indiya kwatankwacin dalar Amurka 195,983,700.00, ya sadaukar ga masu fama da lalurar cutar daji wato kansa da ke zaune a Mumbai da Kolkata.

Shilpa Shetty

Hakkin mallakar hoto India.com

Jarumar da ta ja hankulan al'umma lokacin da ta ci gasar Big Brother na Birtaniya da aka yi a 2007.

Ta samu fam dubu 100 wanda ya yi kusan crore 1, kwatankwacin dala miliyan 13 ga kungiyoyin da ke wayar da kai ga masu cutar da ke karya garkuwar jiki ko kuma sida.

Salman Khan

Hakkin mallakar hoto Washington Post

Salman Khan, dama tuni ya yi alkawarin cewa duk kudin da zai samu daga fim, to kaso 10 cikin 100 na kudin ne kawai zai dauka ya yi amfani da su don kashin kansa, amma sauran kaso 90 cikin 100, zai rinka bayarwa ne ga mabukata ko kuma wasu masu dauke da wata lalura da suke neman taimako.

Ba sau daya ba sau biyu ba, Salman Khan ya sha taimakawa wasu daga cikin abokan aikinsa ma da suka shiga wata damuwa ta rashin kudi ko kuma suke fama da wata lalura.

Nana Patekar

Hakkin mallakar hoto Deccan Chronicle

Jarumin wanda har yanzu ke zaune a gidan da bai taka kara ya karya ba tare da iyalansa, ya na sadaukar da kaso 90 cikin 100 na kudin da ya ke samu a fim ga mabukata.

Duk da irin fitattun fina-finan da Nana Patekar ke yi, kudadensa ba sa gabansa, sai dai taimako ga marassa karfi.

Yana rayuwa dai-dai misali domin ba bu abin da ya rasa, amma bai tara wata dukiya ta zao a gani ba, saboda duk ya sadaukar.

Sonam Kapoor

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Matashiyar jarumar ta na bayar da kyauta ga abubuwan da ta mallaka, ba kudi ba kawai hatta kayanta na sawa.

Akwai lokacin da Sonam ta kwashe kayanta na sawa gaba daya ta kai gidan marayu domin a raba wa wadanda za su iya sanya wa.

Abin ta bai rufe mata idanu ba, haka kudinta na fim ma idan ta yi, ta kan kwashi na kaso ta ba wa mabukata ko wasu masu lalurar rashin lafiya domin su yi magani.

Labarai masu alaka