Chelsea na daf da daukar Gonzalo Higuain

Gonzalo Higuain Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Chelsea ta kusa kulla yarjejeniyar daukar aron dan wasan tawagar kwallon kafar Argentina, Gonzalo Higuain.

Higuain wanda ke wasa aro a AC Milan daga Juventus ya ci kwallo daya a wasa 12 da ya buga wa Milan a bana.

Sai dai kwallo 36 da ya ci a wasa 35 a Serie A da ya yi a Napoli karkashin Maurizio Sarri a 2015/16 ya sa Chelsea ta sake shawara kan daukar duk dan wasan da ya cika shekara 30 da haihuwa.

Ana sa ran Chelsea za ta dauki aron dan wasan daga Milan zuwa karshen kakar bana, bayan da kungiyar ke karancin 'yan wasan da ke cin kwallaye.

Kocin Chelsea, Sarri ya ce ko da sun dauki dan wasan ba zai buga musu karawar League Cup wasan daf da karshe da za ta yi da Tottenham a ranar Alhamis a Stamford Bridge ba.

Tottenham ta yi nasarar cin Chelsea 1-0 a wasan farko a League Cup da suka fafata a Wembley.

Labarai masu alaka