Trump ya amince da dan adawa a matsayin shugaban kasar Venezuela

Mr Guaidó ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko ranar Laraba Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr Guaidó ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko ranar Laraba

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya amince da jagoran 'yan hamayyar Venezuela Juan Guaidó a matsayin shugaban riko na kasar.

Ya dauki wannan mataki ne jim adan bayan jagoran 'yan hamayyar mai shekara 35 a duniya ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko a birnin Caracas ranar Laraba.

Kasashen kudancin Amurka da dama, cikin har da Brazil, Colombia da kuma Peru, sun amince da Mr Guaidó a matsayin sahihin shugaban kasar ta Venezuela.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da 'yan kasar ke zanga-zangar kyamar gwamnatin Shugaba Nicolás Maduro wanda karkashin mulkinsa tattalin arzikin kasar ke ci gaba da tabarbarewa.

Venezuela na fama da hauhawar farashin kayayyaki da daukewar wutar lantarki da kuma karancin abubuwan more rayuwa lamarin da ya jefa miliyoyin 'yan kasar cikin kunci.

A farkon watan nan ne aka rantsar da Mr Maduro domin yin wa'adi na biyu na mulki, bayan zabe da aka gudanar wanda 'yan hamayya suka kauracewa, wanda kuma aka yi zargin an tafka magudi.

Da yake yin raddi kan matsayar da Mr Trump ya dauka ta amincewa da jagoran 'yan hammayar a matsayin shugaban kasa, Mr Maduro ya yanke huldar jakadanci da Amurka sannan ya bai wa jami'an jakadancin Amurka kwana biyu su fice daga Venezuela.

Ya zargi Amurka da yunkurin mulkar Venezuela daga gefe yana mai zargin 'yan hamayyar da yunkurin juyin mulki.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dubban daruruwan 'yan kasar Venezuela ke zanga-zangar kyamar gwamnatinsu

Labarai masu alaka