Oby Ezekwesili ta janye daga takarar shugabancin Najeriya #BBCNigeria2019

Oby Ezekwesili Hakkin mallakar hoto Twitter/@obyezeks
Image caption Oby Ezekwesili ta ce za ta shiga gammayar jam'iyyun da za su kayar da APC ko PDP

'Yar takarar shugabancin Najeriya ta jam'iyyar ACPN, Oby Ezekwesili, ta janye daga takarar shugabancin Najeriya.

A wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter, tsohuwar mataimakiyar shugaban babban bankin duniyar, ta ce ta dauki matakin ne bayan ta tattauna da abokan shawarta na ciki da wajen kasar.

A cewarta, yanzu za ta mayar da hankali ne wurin shiga gamayyar jam'iyyun da za su kwace mulki daga jam'iyyar APC ko kuma su hana jam'iyyar PDP cin zabe.

"Na kwashe sama da wata uku ina yin tattaunawar sirri da sauran 'yan takara da zummar hada gamayyar jam'iyyun da za a bai wa 'yan Najeriya damar yin zabe ba tare da sun iyakance zabin nasu kan jam'iyyar APC ko PDP ba," in ji Mrs Oby.

Ta kara da cewa wannnan gamayya ta yi karfin da ba a taba samun wata gamayyar jam'iyyu ta yi ba a tarihin Najeriya.

Masu sharhi a kan sha'anin siyasa na ganin ko da Mrs Oby ta fafata a zaben ba za ta yi tasiri ba, sai dai yanzu za a zuba ido a gani ko gammayar jam'iyyun za ta iya kwace mulki a hannun APC ko kuma ta hana PDP lashe zabe.