Matar da ke bayar da gudummawar bahayanta

Claudia Campenella Hakkin mallakar hoto Claudia Campenella
Image caption Claudia na so ta karfafa wa sauran mutane gwiwa don su fara bayar da gudummawar bahayansu

Claudia Campenella 'yar shekara 31 daliba ce mai tamakawa a fannin gudanarwa a wata jami'a a Burtaniya, inda take bada gudummawar bahayanta a lokacin da take da sarari.

Campenella ta bayyana cewa, 'wasu daga cikin kawayena na ganin hakan a matsayin abin kyama, amma baya damu na.

Abu ne mai sauki bayar da gudummawa, ina so ne in taimaka wajen binciken ilimi ta fannin lafiya, ina jin dadin taimakawa."

Ana saka bayan gidan Claudia cikin kwano dauke da kwari inda yake taimakawa marasa lafiya su samu lafiyar hanji.

Claudia ta san cewa gudummawar ta na da matukar amfani shiyasa take bayarwa- amma bayan gidanta na musamman ne?

Masana kimiyya sun bayyana cewa bayan gidan wasu yana dauke da kwayoyin cuta masu warkar da cuta musamman cutar hanji.

Claudia ta ce tana so ne ta zama mai bada gudummawar saboda ta karanta cewa bayan gidan marasa ta'ammali da naman dabbobi su ne bayan gidan su ke zama haka.

Amma babu wata cikakkiyar hujja dake nuna cewa bayan gidan marasa ta'ammali da naman dabobbi yafi na sauran mutane, sai dai masana suna bincike akan ko akwai bambanci a bayan gida.

Akwai miliyoyin kwayoyin halitta a cikin hanjinmu da ke rayuwa kamar al'umma guda.

Duk da dai dashen bayan gida sabon bangare ne a kiwon lafiya, bayanai daga wasu bincike-bincike da aka yi sun nuna cewa akwai mutanen da bayan gidansu ya ke da matukar muhimmanci wajen yin dashe.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Claudia Campenella

Claudia na so mutane su sauya tunaninsu kan bayar da gudummawar bahaya.

"Abu ne mai saukin gaske.

"Ina zuba sabon bahaya a 'yar karamar roba daga gida in kai asibiti, ba abu ne mai wahala ba", inji Claudia.

Labarai masu alaka