Mikel Obi ya koma Middlesbrough

John Mikel Obi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption John Mikel Obi ya yi wa Najeriya kyaftin a gasar cin kofin duniya a shekarar 2018

Middlesbrough ta dauki tsohon dan wasan Chelsea John Mikel Obi a wata yarjejeniya har zuwa karshen kakar bana.

Dan wasan mai shekara 31 wanda kuma ya lashe kofin zakarun Turai tare da Chelsea a shekarar 2012, ya kasance ba tare da kungiya ba bayan da ya bar kungiuyar Tianjin Teda ta kasar China.

Mikel ya buga wa Chelsea wasanni 249 a tsawon shakara 11 da ya yi kafin ya bar kungiyar shakaru biyu da suka wuce.

Ya kuma lashe kofunan league guda biyu da kofin kalubale na FA guda uku da kuma gasar Europa a shekarar 2013.

"Na yi farin cikin kawo shi. Kwararren dan wasa ne mai nagarta", in ji kocin Middlesbrough Tony Pulis kamar yadda ya fada wa shafin Intanet na kulob din.

"Yana da gogewa kuma zai so ya kasance tare da mu domin cimma nasarori".

Dan wasan tsakiyar na Najeriya ya buga wa kasarsa wasanni 85. Yana cikin tawagar 'yan wasan Najeriyar a gasar cin kofin duniya guda biyu sannan kuma ya taimaka wa kasar lashe gasar cin kofin kasashen Afirka a sherkarar 2013.

Kuma yana cikin manyan 'yan wasan Najeriya da suka lashe tagulla a gasar Olympics a shekarar 2016 a birnin Rio na Brazil.

Labarai masu alaka