Zaben 2019: Ra'ayoyin jama'a kan matar da aka saka don Buhari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari hirar da BBC ta yi da mijin da ya saki matarsa don Buhari

Mun samu ra'ayoyin dimbin jama'a bayan wallafa labarin wata mata da mijinta ya sake ta don za ta zabi Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ya yi wa matarsa Hafsat Suleiman saki biyu ne bayan da ta sha alwashin cewa "ita Shugaba Muhammadu Buhari za ta zaba a zaben 2019."

Ya ce har sai da maganar ta kai gaban iyayenta, inda daga nan ne sai ya yanke hukuncin sakinta wanda kuma "har ya balla mata hakori," a cewarsa.

Jama'a sun rika bayyana mabambantan ra'ayi game da labarin musamman lokacin da muka wallafa shi a shafinmu na Facebook.

Yayin da wasu suke ganin wautar mijin, wasu tausayawa matar suka rika yi inda aka samu wadanda suka bayyana sha'awarsu ta neman aurenta idan ta kammala idda.

Hakkin mallakar hoto Facebook

Har ila yau mun samu kiraye-kiraye waya daga wurare daban-daban inda jama'a suke neman lambar Hafsat.

Hakkin mallakar hoto Facebook

Akwai wani da ya kwatanta abin daya faru da Hafsat da yadda uwargidan shugaban kasa , Aisha Buhari, ta gargadi mijinta cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba, idan har al'amura suka ci gaba da tafiya a haka.

Hakkin mallakar hoto Facebook