Yadda kango ya zama mazaunin fursunonin siyasa a Venezuela

An dai gina El helicoide ne a shekarun 1950 a daidai lokacin da Venezuela ke ganiyar samun kudin shiga ta hanyar man fetur. Hakkin mallakar hoto Archivo FotografĂ­a Urbana / Proyecto Helicoide
Image caption An dai gina El helicoide ne a shekarun 1950 a daidai lokacin da Venezuela ke ganiyar samun kudin shiga ta hanyar man fetur.

A tsakiyar Caracas babban birnin Venezuela, akwai wani katafaren tsohon gini mai tsawon gaske wanda yake cikin unguwar marasa galihu.

El Helicoide gini ne wanda yake alamta kasa mai arziki da cigaba.

Yanzu dai wannan gini ya zama mazaunin gawurtattun 'yan fursuna.

An dai gina El helicoide ne a shekarun 1950 a daidai lokacin da Venezuela ke ganiyar samun kudin shiga ta hanyar man fetur.

Shugaban kasar na wancan lokaci Marcoz Perez Jimenez ya fara gina wurin domin ya nuna kasar a matsayin mai rajin ci gaba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ginin ya tashi daga rukunin shaguna zuwa fursuna

Venezuela kasa ce da ta shiga mulkin soja na kama karya a 1948.

Ana da burin El Helicoide ya zama na farko a duniya ta fannin siyayya a shaguna, inda a wannan ginin akwai sama da shaguna 300 da aka gina domin siyar da kayan sawa.

Ginin na da girman da za a iya hangensa daga ko ina a birnin.

Wannan gini ne mai matukar daraja, babu gini irin sa a yankin Latin Amurka, inji Dakta Blackmore.

An yi ginin ne da niyyar za a samu otal a ciki, wurin saukar jirgi mai saukar ungulu, da sauran kayattatun abubuwa.

Amma an tsige shugaba Perez Jimenez a 1958 inda wannan burin na sa na gina El Helicoide ya zama wurin kwatance a duniya yabi ruwa.

Hakkin mallakar hoto Archivo FotografĂ­a Urbana / Proyecto Helicoide
Image caption This space-age building was carved into the rock with ramps spiralling up past 300 planned boutiques

Wurin ya zama kango

Wurin ya shafe shekaru a matsayin kango, anyi ayyuka domin ganin cewa an gina wurin amma abin yaci tura.

A shekarun 1980, gwamnatin kasar ta fara mayar da wasu daga cikin ma'aikatun kasar zuwa El Helicoide, inda har aka mayar da hukumar tattara bayanan sirri ta kasar wannan ginin.

Tun bayan lokacin ne, ginin yazama wani wuri da ake shakka saboda irin nau'in mutanen da ake tsarewa da suka hada da manyan masu laifuka da 'yan siyasa.

BBC tayi hira da wasu tsoffin 'yan fursuna da suka zauna a ginin, iyalansu da lauyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma wasu tsoffin masu gadin ginin guda biyu domin fito da bayanai kan yadda ake gudanar da rayuwa a wannan wuri.

Sun bukaci da mu sakaya sunayensu domin tsoron kada gwamnati ta gallaza wa iyalansu.

Rosmit Mantilla dan shekara 32, ya isa El Helicoide ne a watan Mayun 2014, yana daga cikin mutane 3000 da aka kama a wata zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Mantilla dan siyasa ne kuma dan gwagwarmaya ne a kasar.

Da ba a tsare shi ba, da watakila yanzu ya zama zababben dan majalisa a Venezuela.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kama dubban 'yan Venezuela a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Matsin tattalin arziki da na siyasa

Gudanar da rayuwa a Venezuela na kara wahala, sakamakon tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki da karancin abinci da magunguna da dai sauran su.

A ginin El Helicoide, za a iya cewa lokacin hayaniya ne, domin kuwa a kullum ana kawo motoci cike da 'yan fursuna.

An tarwatsa 'yan makaranta, 'yan gwagwarmayar siyasa, harda yara ma da suka zo suna zanga-zanga a gaban ginin.

An zargi Mantilla da taimakawa wajen daukar nauyin wannan zanga-zangar, batun kuma da ya musanta.

Manuel, tsohon gandiroba ne wanda ya tuna da rayuwar Mantilla a wannan wuri.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsoratar da mutane

Daya daga cikin tsoffin ma'aikatan wurin ya shaidawa BBC cewa: ''Ana kama mutane ne domin a tsoratar da jama'a."

"Kuma ina tunanin anyi haka ne saboda a duk lokacin da ake zanga-zanga a Venezuela, mutane da dama suna tsoron kada a kama su."

'Yan fursuna a El Helicoide suna jira kusan watanni da dama kafin a gurfanar dasu gaban kotu.

Image caption A lokacin da yawan 'yan fursunan yake karuwa ai da aka kara gyara wurin zama dominsu

'Guantanamo'

A lokacin da Mantilla ya isa El Helicoide a 2014, ya bayyana cewa mutane 50 ne kadai aka tsare a wurin. Bayan shekaru biyu, sai suka zama 300.

A lokacin da yawan 'yan fursunan ke karuwa, sai da aka kara gyara wurin zama dominsu.

Ofisoshi da makewayi da sauran wuraren da aka gina domin su zama shaguna na kasaita amma an mayar dasu dakunan fursuna.

'Yan fursunan sun bai wa dakunan zaman su sunaye kamar Fish Tank, Little Tiger, Little Hell da Guantanamo.

Amma wanda ya fi muni a ciki shi ne Guantanamo.

Guantanamo tsohon dakin ajiya ne kuma yana da girman kafa 12, kuma yana daukar fursunoni kusan 50.

Guantanamo yana da zafi, babu sararin wurin shigar iska yanda ya kamata.

Mantilla ya kwatanta Guantanamo a matsayin dakin da ba wuta ba ruwa babu makewayi kuma babu gadaje sannan ba a gyara shi kuma an bata bangon dakin da fitsari da kuma jini.

Ya shaidawa BBC cewa fursunonin suna daukar makwanni batare da wanka ba, suna fitsari a cikin roba, suna bayan gida a cikin leda.

Image caption 'Yan fursunan sun baiwa dakunan zaman su sunaye, Amma wanda yafi muni a ciki shine Guantanamo.

Azabtarwa

Amma ukuba ba ita ce kadai abin da ake tsoro a El Helicoide ba.

Duk sauran tsaffin gandurobobin da suka yi hira da BBC a kan yadda suka san fursunar El Helicoide sun nuna cewa ana azabtar da 'yan fursuna domin su amsa laifin su.

Wani tsohon dan fursuna mai suna Carlos ya shaidawa BBC cewa: ''Sun rufe kaina da wata jaka, sun mani dan karen duka, sunyi amfani da lantarki suka azabtar da 'yan marainana da cikina .''

Haka wani tsohon fursuna mai suna Luis ya bayyana cewa: ''An rufe kaina sai naji wani jami'insu yana cewa: "ku kawo bindigar nan, sai mun kashe ka."

"Suna ta dariya, suna cewa, "saura harsashe daya, bari mu gani ko kana da sa'a." ina jin gindin bindiga kirar pistol a bisa kaina...ina ji suna harba kunamar, sun harba yafi a kirga."

A watan Mayun 2018, fursunoni a El Helicoide sun yi zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin zaman fursunan.

An saki da dama cikin fursunonin haka kuma an yi alkawurra da dama domin inganta yanayin fursunan.

Amma kamar yadda wasu daga cikin fursunonin suka shaida, ba a yi wani abin a zo a gani ba domin inganta wurin zaman na su.

BBC dai ta dade tana tuntubar hukumomi a Venezuela inda suka mika koke a kan irin abubuwan dake faruwa a El Helicoide.

Labarai masu alaka