An rantsar da sabon shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Congo

Felix Tshisekedi waving after he was announced as winner of the elections in Kinshasa, DR Congo - 10 January 2019 Hakkin mallakar hoto Reuters

An rantsar da sabon shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Felix Tshiseked a ranar Alhamis.

Ya shaida wa manema labarai a wajen bikin rantsuwar cewa zai hada kan 'yan Congo.

Mr Tshisekedi ya dan yi fama da gajeriyar rashin lafiya jim kadan kafin ya sha rantsuwar kama mulki.

Daga baya mai magana da yawunsa ya gayawa kamfanin dilancin labarai na Reuters cewa rigar silken da ya sanya ce ta matse shi da yawa.

Ya gaji Joseph Kabila a mika mulki na farko da aka yi cikin lumana cikin shekara 60 da suka gabata, duk da cewa mutane da dama suna tababar samun nasarar tasa.

Sabon shugaban ya yabi tsohon shugaban saboda bar masa mulki da ya yi.

Shugaban kasar Uhuru Kenyatta ne kawai wanda ya halarci bikin rantsuwar cikin shugabannin nahiyar Afirka 17 da aka gayyata.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

An san sabon shugaban a matsayin dan marigayi fitaccen jagoran hamayya Etienne Tshisekedi, wanda ake ganinsa a matsayin daya daga cikin mutane masu muhimmanci da ke rajin kare dimokradiyya na kasar Congo

An kirkiri Jam'iyyar UDPS ta Shugaba Tshisekedi a 1982 kuma mahaifinsa ne ya kirkire ta, wanda ya mayar da ita babbar jam'iyyar adawa.

Amma Shugaba Tshisekedi mai shekara 55, ya yi ta jaddada cewa ba burinsa ya yi adawa da mahaifinsa ba.

Labarai masu alaka