Ana zanga-zangar da ba a taba yin irin ta ba a Sudan

'Yan sanda sun jefa hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga-zangar a Khartoum. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda sun jefa hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga-zangar a Khartoum.

Jami'an tsaro sun yi arangama da masu zanga-zanga a Khartoum, babban birnin Sudan a yayin da ake gangamin kyamar gwamnati a duk fadin kasar.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun jefa kwanso-kwanson hayaki mai sanya kwalla da zummar tarwatsa masu zanga-zangar.

Kungiyoyin likitoci da injiniyoyi da kuma malaman makaranta wadanda ke cikin masu zanga-zangar sun ce suna gudanar da ita a akalla wurare 50 a duk fadin Sudan.

A watan jiya ne aka soma zanga-zangar a kan matsin tattalin arziki, sai dai yanzu masu yin ta sun mayar da hankali ne kan bukatar sauke Omar al-Bashir daga mulki.

'Yar jarida Zeinab Mohammed Salih ta shaida wa BBC ranar Alhamis cewa wannan ita ce zanga-zanga mafi muni da aka yi a kasar a tarihinta.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun jefa hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga-zangar a wurare daban-daban da ke da makwabtaka da Khartoum.

Tun lokacin da aka soma zanga-zangar, jami'ai sun ce akalla mutum 26 ne suka mutu, amma kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce fiye da mutum 40 ne suka mutu.

Labarai masu alaka