Zaben 2019: Atiku ya gama cin zaben 2019 – Buba Galadima

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Buhari bai taba ba ni koda sisin kwabo ba'

Daya daga cikin manyan masu goyon bayan takarar Atiku Abubakar, Injiniya Buba Galadima, ya ce dan takararsu a zaben 2019 ya gama lashe zaben saboda yadda ya samu karbuwa wajen al'ummar Najeriya.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis.

Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP zai fafata ne da Shugaba Muhammadu Buhari na APC, wanda ke neman wa'adi na biyu.

Buba Galadima ya ce suna godiya ga 'yan Najeriya saboda irin goyon bayan da suke samu a tarukan yakin neman zabe da ke gudana a fadin kasar.

"Kuma idan dai kuri'ar dan Najeriya ita za ta tabbatar da cin zabe, to mun gama cin zabe," in ji shi.

Har ila yau, ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar ya fi Shugaba Buhari tara jama'a a lokutan yakin neman zabe.

Buba Galadima wanda a baya na hannun daman Shugaba Buhari ne kafin ya fara mara wa Atiku baya, ya yi zargin cewa Buhari yana amfani da kudi ne wajen tara jama'a.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa cewa kudi ne suka sa shi komawa wurin Atiku Abubakar, inda ya ce: "Buhari bai taba ba ni koda sisin kwabo ba, to idan shi a lokacin bai ba ni ba, to ya za a ce a yanzu wani zai saye ni."