Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya

Wasu daga cikin hotunan 'yan Afirka daga sassan duniya da nahiyara wannan makon.

Masu son hango yadda ake rantsar da sabon shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun hau kan bishiyoyi a filin fadar shugaban kasar a Kinshasa... Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu son hango yadda ake rantsar da sabon shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun hau kan bishiyoyi a filin fadar shugaban kasar a Kinshasa...
Drummers in the grounds of the presidential palace in Kinshasa, DR Congo - Thursday 24 January 2019 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Bikin rantsar da shugaban kasar wanda shi ne karon farko da aka mika mulki cikin kwanciyar hankali a cikin shekara 60.
Ethiopia's Prime Minister Abiy Ahmed and Pope Francis during a private audience at the Vatican - Monday 21 January 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firayim ministan Habasha Abiy Ahmed na nuna wa Fafaroma Francis wani zanin gargajiya ranar Litinin.
Traditionally attired Ethiopian Orthodox Christians use smart phones - Friday 18 January 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu kiristoci 'yan Habasha na amfani da wayar hannu ranar Juma'a a bikin gargajiya na Timket a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
The facade of Zeitz Museum of Contemporary Art Africa in Cape Town, South Africa - Tuesday 22 January 2019 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani gini da ake ajiye kayayyakin mutanen zamanin da a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.
Nan pierced with spikes, flowers and limes dances during the annual Hindu Thaipoosam Kavady near Durban, South Africa - Monday 21 January 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A birnin Durban da ke Afirka ta Kudu, wani mutum ya huda jikinsa da karafuna inda ya jera furanni da lemon tsami yana rawa a bikin addinin Hindu na Thaipoosam Kavady ranar Litinin.
A Hindu worshipper carries a "kavadi" or offering on his shoulders Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mabiyin addinin Hindu ya dauki jerin furanni da ake kira "kvadi" a bikin na mabiya addinin Hindu
Mourners at a church in Nairobi, Kenya - Wednesday 23 January 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu masu alhini a lokacin jana'izar mutanen da suka mutu a harin da aka kai a otal din Dusit a Nairobi babban birnin Kenya.
Man carrying empty jerry cans in Nairobi, Kenya - Friday 18 January 2019 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A Nairobi ran Juma'a, wani mutum ya dauki jarkoki kan kafadunsa a unguwar Eastleigh.
The slum of Makoko in Lagos, Nigeria - Wednesday Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Unguwar Makoko da ke Legas. An gina wannan unguwar marasa galihun a gefen tekun na Legas.
A boy holding up secondhand clothes for sale in Kara-Isheri in Ogun State, Nigeria - Tuesday 22 January 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A jihar Ogun da ke kudancin Najeriya, wani matashi ya rike rigar gwanjo ranar Talata.
A Malian holding hay at a farm in Gironde-sur-Dropt, France - Tuesday 22 January 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani dan ci rani dan asalin Mali wanda ke aikin kula da raguna a wata gona a arewa maso yammacin Faransa ranar Talata.

Hotuna: AFP, EPA da Reuters