Buhari ya cire babban Alkalin Najeriya, Walter Onnoghen

Walter Onnoghen, ya zama alkalin akalai a 2016 Hakkin mallakar hoto CHANNELS
Image caption Walter Onnoghen, ya zama alkalin akalai a 2016

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen har sai an gama shari'ar da ake yi da shi a kotun da'ar ma'aikata (CCT).Shugaba Buhari ya sanar da dakatarwar ne a fadar shugaban kasa dake a Abuja.

Ya bayyana cewa kotun da'ar ma'aikata ce ta bayar da umarni a dakatar da shi har sai an gama gudanar da shari'arsa.

Shugaban kasan ya rantsar da Mai shari'a Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukaddashin alkalan alkalan Najeriya.

Mai shari'a Ibrahim Tanko dai dan asalin jihar Bauchi ne kuma shi ne ke da mafi girman mukami a kotun kolin Najeriya.

Mako biyu da ya wuce ne gwamnatin Najeriya ta bukaci Walter Onnoghen ya dakatar da aikinsa kan zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Kotun da'ar ma'aikata, ta bukaci alkalin ya gurfana a gabanta ranar Litinin 14 ga watan Janairu.

Sai dai bai bayyana a gaban kotun ba don sauraron shari'ar.

Laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

Labarai masu alaka