Kun san me doka ta ce kan dakatar da Alkalin Alkalai?

'Kotu ce ta ba shugaba Buhari umurnin dakatar da Onnoghen' Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/FEMI ADESINA

Masana shari'a na ci gaba da sharhi da kuma fassara doka bayan matakin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dauka na nada sabon alkalin alkalan kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki matakin ne bayan samu wani umurni daga kotun da'ar ma'aikata ta kasar, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.

Inda kotun ta bukaci shugaban kasar ya dakatar da Walter Samuel Nkanu Onnoghen har sai an gama shari'ar da ake yi masa kotun ta da'ar ma'aikata (CCT).

BBC ta tuntubi Malam Muhammad Shu'aib, lauya mai zaman kansa a Abuja, inda aka tambaye shi ko shugaban kasar na da hurumin dakatar da alkalin alakalan kasar?

Lauyan ya ce babu wata doka da ta bai wa shugaban kasar hurumin yin gaban-kansa wajen dakatar da alkalin alkalan.

Sai dai ya ce shugaban kasar bai saba wa doka ba kasancewar ya yi amfani ne da umurnin kotun wajen dakatar da Walter Onnoghen.

A cewar sa 'Ba wai kundin tsarin mulki ba ne suke takama da shi wajen dakatar da wannan babban joji (Walter Onnoghen), oda (Umurni) ne kotu ta bayar cewa a dakatar da shi.'

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/FEMI ADESINA

Shugaban kasan ya rantsar da Mai shari'a Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukaddashin alkalan alkalan Najeriya.

Mako biyu da suka wuce ne gwamnatin Najeriya ta bukaci Walter Onnoghen ya dakatar da aikinsa kan zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Hakkin mallakar hoto NATIONAL JUDICIAL COUNCIL

Kotun da'ar ma'aikata, ta bukaci alkalin ya gurfana a gabanta ranar Litinin 14 ga watan Janairu.

Sai dai bai bayyana a gaban kotun ba don sauraron shari'ar.

Laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.