Da gaske Aisha Buhari ta yi Allah wadai da dakatar da Onnoghen?

Aisha Buhari Hakkin mallakar hoto Presidency

Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta karyata wasu rahotanni da suka ce ta yi Allah wadai da dakatar da Alkalin Alkalan kasar Walter Onnoghen.

Ta dai bayyana hakan ne a wata sanarwa da daraktan watsa labaranta Mista Suleiman Haruna ya fitar inda sanarwar ta bayyana cewa labarin da ake yadawa a kafofin sadarwa cewa ta yi tsokaci kan dakatar Onnoghen ba gaskiya ba ne.

"Yana da kyau a sanar da 'yan Najeriya cewa uwar gidan shugaban kasa ba ta fito ta yi magana ba kan wannan batun, don haka karya ne," in ji sanarwar.

A ranar Jumma'a ne dai Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalan kasar Walter Onnoghen har sai an gama shari'ar da ake yi da shi a kotun da'ar ma'aikata (CCT).

Shugaban ya bayyana cewa kotun da'ar ma'aikata ce ta bayar da umarni a dakatar da shi har sai an gama gudanar da shari'arsa.

A kwanakin baya an dai ta samun suka daga wurin uwar gidan shugaban a kan yadda ta ke ganin mai gidanta ke gudanar da mulki a kasar.

Ta yi zargin cewa akwai mutane kalilan da sukayi kane-kane ga harkokin gudanar da kasar.

A kwanakin baya ma ta soki jam'iyya mai mulki a kasar APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwani a bara inda ta bayyana cewa jam'iyyar ba ta yi adalci ba.

Labarai masu alaka