CJF Onnoghen: Lauyoyi sun yi zanga-zanga kan dakatar da shi a Abuja

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hussaini Saraki: Lauya mai goyon bayan matakin Buhari

Wadansu lauyoyi sun yi zanga-zanga kan matakin dakatar Babban Alkalin Najeriya Walter Onnoghen a gaban hedikwatar kungiyarsu (NBA) a Abuja ranar Litinin.

Masu zanga-zangar sun ce suna so ne Shugaba Muhammadu Buhari ya soke matakin dakatar da babban alkalin kasar.

Sai dai akwai kuma wasu lauyoyi da suka nuna goyon bayansu game da dakatar da Mista Onnoghen.

A ranar Juma'a ne Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen bayan kotun da'ar ma'aikata (CCT) ta umarce shi da ya yi hakan saboda tuhumarsa da kin bayyana kadakorinsa.

Har ilayau shugaban ya rantsar da Mai Shari'a Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukaddashin babban alkalin kasar.

Lauyoyin sun bukaci kungiyar NBA da ta fara yajin aiki kuma hukumar da ke kula da bangaren shari'ar da ta dakatar da sabon mukaddashin Alkalin Alkalin.

Yayin da suke zanga-zanga, an samu wani ayarin masu zanga-zanga da ya isa wurin, inda suke goyon bayan matakin Shugaba Buhari na dakatar da Onnoghen.

A safiyar ranar Litinin, an girke 'yan sanda a gaban hedikwatar kungiyar NBA, inda mambobin suka yi wani taron don tattauna batun dakatar da Alkalin Alkalin.

Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption An girke 'yan sanda a gaban hedikwatar kungiyar NBA da ke Abuja ranar Litinin

Kungiyar lauyoyin ta kira wani taron gaggawa a ranar Litinin, bayan Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen.

Daya daga cikin lauyoyin da suka shiga zanga-zangar, sun ce Shugaba Buhari bai bi ka'ida ba wajen dakatar da alkalin.

Ya ce gwamnati ta nuna son kai don ya kamata ne kafin shugaban ya dauki matakin sai ya rubuta wa majalisar dattawan kasar.

Image caption Hedkwatar NBA a Abuja