Onnoghen: Kawunan 'yan majalisa sun rabu kan gurfanar da Buhari a kotu

Majalisar dattawan Najeriya Hakkin mallakar hoto NASS

'Yan jam'iyyar APC da ke majalisar dattawan Najeriya sun barratan kansu daga matakin da shugabannin majalisar suka dauka na kai shugaban kasar Muhammadu Buhari kotu saboda dakatar da alkalin alkalan kasar.

Ranar Litinin ne majalisar dattawan ta shigar da kara a kotun kolin kasar inda ta bukace ta yanke hukunci kan ko ya dace Shugaba Buhari ya dakatar da alkalin alkalan Walter Onnoghen.

Sanarwar da Yusuph Olaniyonu, kakakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya fitar ta bayyana cewa sun shigar da karar ne "muna neman kotun ne da ta yi mana bayani a kan ko Shugaba Buhari na da hurumin cire Mista Onnoghen."

Sanarwar ta bayyana dage zaman da aka shirya yi a ranar Talata saboda da ma a kan batun cire Mista Onnoghen za a yi.

Sai dai wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Ahmed Lawan, ya fitar ranar Litinin da yamma ta ce shugabannin majalisar basu tunytube su ba kafin su kai Shugaba Buhari kotu.

"Muna so muna sanar cewa majalisar dattawa bata dauki wannan matsaya ta zuwa kotun koli ba. don haka mu 'yan jam'iyyar APC muna barranta kanmu wannan batu."

Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen ne bisa shawarar kotun da'ar ma'aikata wacce ta samu alkalin alkalan da laifin kin bayyana cikakkun kaddarorinsa lokacin da aka nada shi kan mukamin a 2017.

Sai dai Mista Onnoghen ya ce ba da gangan ya yi hakan ba, yana mai cewa mantawa ya yi.

Kungiyar lauyoyin kasar dai ta yi zanga-zanga kan matakin da Shugaba Buhari ya dauka kan Mista Onnoghen inda ta bukaci mambobinta da su kauracewa kotu tsawon kwana biyu.

Sai dai wasu daga cikin 'yan kungiyar sun ce ba za su fasa zuwa kotu ba.

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma tarayyar turai sun yi allawadai da dakatar da Mista Onnoghen.

Sai dai gwamnatin ta ce ba za ta amince da katsalandan daga kasashen waje cikin harkokin gidanta ba.