Matsafa sun yanke sassan jikin wasu yara a Tanzania

Map showing Tanzania

Hukumomi a Tanzania sun ce an kashe yara shida a kudu maso yammacin kasar sannan aka cire kunnuwa da hakoransu.

Kazalika an gano cewa an cire yatsun yaran, wadanda shekarunsu suka kama da shida zuwa tara.

Kwamishiniyar lardin Njombe Ruth Msafiri ta ce "An yi hakan ne domin yin tsafi da sassan jikin nasu kuma wasu na ganin za su zama attajirai idan suka yi tsafi da sassan jiki."

'Yan sandan sun tsare wani mutum wanda dan uwa ne ga uku daga cikin yaran, bisa zargi da hannu a kisan su.

Yara goma ne suka bata a lardin Njombe tun farkon watan Disamba ko da yake an gano hudu da ransu.

Wakilan BBC sun ce matsafa ne suke sanya wa a kashe yara sannan a cire wasu sassan jikinsu domin yin asirin da wasu ke gani zai sa su zama attajirai.

Kwamishiniyar ta shaida wa BBC cewa "Muna kira ga iyaye da su sanya ido sosai kan yaransu sannan su rika gaya musu inda za su idan sun fita."

An sace yaran ne daga gidajensu da tsakar dare lokacin iyayensu sun tafi kasuwa inda suke kasuwanci.

Labarai masu alaka

Karin bayani