An kama shugaban 'yan hamayyar Kamaru

An kulle Maurice Kamto tare da wasu 'yan jam'iyyar biyu a birnin Douala. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kulle Maurice Kamto tare da wasu 'yan jam'iyyar biyu a birnin Douala

Babbar jam'iyyar hamayya a Kamaru ta ce an kama shugabanta a daidai lokacin da ake ci gaba da tarzoma kan sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar da ta wuce.

The Movement for the Rebirth of Cameroon (MRC) ta ce an kulle Maurice Kamto tare da wasu 'yan jam'iyyar biyu a birnin Douala.

Mr Kamto ya yi kira ga masu zanga-zanga da su shiga jerin tarzomar da aka yi ranar Asabar ta makon jiya, wacce jami'an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla da harsasai masu kisa kan masu tarzomar.

Shugaba Paul Biya, wanda ya kashe shekara 36 yanba mulkin Kamaru, ya lashe zabe karo na bakwai a watan Oktoba.

Labarai masu alaka