Ba don kudi nake goyon bayan Atiku ba
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sani Danja: 'Abin da ya sa nake goyon bayan Atiku a zaben 2019'

  • Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da dan wasan.

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Sani Musa Danja, ya ce ba don kudi yake goyon bayan dan takarar shugabancin Najeriya Atiku Abubakar ba.

Jarumin ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC a Kaduna, inda ya ce duk abin da suke yi "ra'ayi ne ya sa muke yi."

Atiku Abubakar, wanda yake takara a jam'iyyar PDP, zai fafata ne da Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, wanda yake neman wa'adi na biyu a zaben watan Fabrairun 2019.

Dan wasan ya ce kashi 85 cikin 100 na masu goyon Atiku suna yi ne don ra'ayin kansu, "ko kuma gajiya da wannan gwamnati ko kuma neman mafita ko kuma saboda rashin jin dadin abubuwan da suka faru shekara uku da suka wuce," in ji shi.

A wani bangare kuma yayi karin haske a kan cece-kucen da ake yi game da mai dakinsa, inda aka ce tana goyon bayan jam'iyya mai mulki APC, shi kuma yana PDP.

Ya ce matarsa "ba ta goyon bayan APC kuma ba ma 'yar siyasa ba ce."

Danja ya ce tana da wata gidauniya da ke tallafa wa jama'a ne wadda ke aiki a wani lokaci tare da uwar gidan gwamnan jihar Kebbi ta APC.

Ana dai ci gaba da samun rabuwar kai musamman a bangaren 'yan wasan Hausa na Kannywood da wasu malaman addini, inda wasu suke goyon bayan dan takarar Buhari wasu kuma suke mara wa Atiku baya.