An wallafa sunayen masu kanjamau 14,000 a intanet

An bayyana cewa 'Yan sanda a kasar suna neman agaji daga kasashen ketare a kan wannan lamari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An bayyana cewa 'yan sanda a kasar suna neman agaji daga kasashen ketare a kan wannan lamari

An wallafa sunayen mutane kusan 14,000 masu dauke da cutar kanjamau (HIV) a shafin intanet a kasar Singapore.

Bayanan da aka wallafa na dauke da sunayen 'yan kasar ta Singapore da baki mazauna kasar.

Sunayen dai wasu takardun sirri ne na kiwon lafiya da ake zargin wani Ba'amurke ne mai dauke da cutar ya sace sunayen ya wallafa.

Wannan kutsen yana zuwa ne watanni kadan bayan wani kutse da aka yi a intanet inda aka sace muhimman bayanai na mutum miliyan daya da rabi a kasar wanda ya hada da na Farai Ministan kasar Lee Hsien Loong.

Sunayen da aka wallafa dai na dauke da bayanai da suka hada da adireshin mutanen, bayanai a kan cutar da suke dauke da ita da sauran bayanai da suka shafi lafiyarsu.

Jami'ai a kasar sun bayyana cewa an kawo cikas ga bayanai a kan sunayen 'yan kasar 5,400 da kuma baki mazauna kasar 8,800.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mikhy Farrera-Brochez, wanda ake zargi da wallafa sunayen

Ko kun san wa ya wallafa sunayen?

Jami'an kasar dai sun bayyana wanda ya wallafa sunayen a matsayin wani Ba'amurke, mai hekara 31, mai suna Mikhy Farrera-Brochez wanda ya taba zama a kasar ta Singapore.

An taba daure Mista Mikhy sakamaon laifin da ya aikata na safarar miyagun kwayoyi da almundahana a shekarar 2016.

Mista Mikhy dai tsohon abokin aikin Ler Tech Siang ne wanda kuma shi ne tsohon shugaban sashen kiwon lafiya na kasar.

Shima Mista Siang an daure shi a kwanakin baya sakamakon taimaka wa Mista Mikhy da ya yi domin sauya bayanan lafiyarsa a kan cutar kanjamau domin ya samu damar shiga kasar.

Labarai masu alaka

Karin bayani