Za a saki daruruwan masu zanga-zanga a Sudan

SUDAN PROTESTERS Hakkin mallakar hoto APF

Hukumomi a Sudan sun bayar da umarnin a saki dukkan wadanda ake tsare da su a lokutan zanga-zangar da aka fara a watan Disambar bara.

Kunguyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam sun ce ana tsare da fiye da mutum dubu daya yayin da gwamnatin kasar ke kokarin kawo karshen zanga zangar kawo karshen mulkin Shugaba Omar el Bashir na tsawon shekara talatin.

Rahotanni na cewa an kashe fiye da mutum 40.

Ma'aikatar watsa labarai ta Sudan ta ce umarnin sakin wadanda ake tsare da su ta fito ne daga shugaban hukumar tsaro da leken asiri na kasar Salah Ghosh.

Akwai jagororin 'yan adawa, da masu rajin kare hakkin dan Adam da 'yan jarida cikin fiye da mutum 1,000 cikin wadanda ake tsare da su tun bayan da aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnati makonni shida da suka gabata.

Amma abu ne mai kamar wuya cewa wannan matakin zai sauya wa masu adawa da Shugaba Omar el Bashir ra'ayi akan kiraye-kirayen da suke yi na ya sauka daga mukaminsa.

Hakkin mallakar hoto Reuters

A yayin da matsalar tattalin arzikin kasar ke kara shiga halin hawula'u, da kuma hasashen cewa shugaban zai so ya sake tsayawa takara a shekara mai zuwa, fusatar da 'yan kasar ke yi kan lamarin sai karuwa ya ke yi.

Abin dubawa a nan shi ne yadda jami'an tsaron kasar za su tunkari masu zanga-zanga a makonni da watanni masu zuwa.

Labarai masu alaka