An daure dan majalisa a kan watsa labaran karya

Alain Lobognon proche de Guillaume Soro - archive Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alain Lobognon

Wata kotu a Ivory Coast ta yanke hukuncin daurin shekara daya kan dan majalisar kasar Alain Lobognon bisa samunsa da laifin watsa labaran karya da yunkurin tayar da zaune tsaye.

Kotun ta kuma ci tarar dan majalisar kudin kasar FCFA 300,000 saboda samunsa da watsa labaran kasar da yunkurin tayar da tarzoma.

An zarge shi da wallafa wasu sakonni a Twitter wadanda ka iya haddasa zanga-zanga.

Sai dai lauyan Alain Lobognon ya ce za su daukaka kara.

Lauyan, Affoussi Lamine Bamba, ya yi zargin cewa an yanke hukuncin ne domin cimma wani buri na siyasa yana mai cewa ''an dauki matakin ne kawai saboda Alain Lobognon yana da alaka ta musamman da shugaban majalisar dokoki Mr Soro Guillaume''.

Wannan lamari na faru ne a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaba Alassane Ouattara da Mr Soro Guillaume.

Ranar Litinin Shugaba Ouattara ya bayyana cewa a watan Fabrairu Mr Guillaume zai sauka daga mukaminsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lamarin na faru ne a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaba Alassane Ouattara da Mr Soro Guillaume.

Labarai masu alaka