Kotu ta hana jagoran 'yan hamayyar Venezuela fita daga kasar

Juan Guaidó in Caracas, 27 January Hakkin mallakar hoto Reuters

Kotun kolin Venezuela ta hana jagoran 'yan hamayyar kasar Juan Guaidó barin kasar sannan ta kwace kaddarorinsa.

Wannan lamari na faruwa ne a yayin da ake ci gaba da fafutuka kan mulkin kasar, bayan Mr Guaidó ya ayyana kansa a matsayin shugaban wucingadi a makon jiya.

Amurka da wasu kasashe na goyon bayansa. Sai dai Russia da wasu kasashe na goyon bayan Shugaba Nicolás Maduro.

A wata hira da ya yi kafafen watsa labarai, Mr Maduro ya ce a shirye yake ya tattauna da 'yan hamayya.

"A shirye nake na zauna a tebirin sulhu da 'yan hamayya domin tattaunawa kan makomar Venezuela," in ji shi, a hirar da ya yi da kamfanin dillanacin labaran Russia RIA Novosti a Caracas.

'Yan hamayya sun yi kira ga magoya bayansu su gudanar da zanga-zangar lumana ta awa biyu da za a yi ranar Laraba. Babu tabbas a kan ko Mr Guaidó zai halarci zanga-zangar.

Wasu kasashen arewaci da kudancin Amurka sun yi watsi da duk wani yunkurin tsoma bakin sojojin waje cikin rikicin kasar ta Venezuela.

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce za su yi amfani da duk wata dama wajen kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Labarai masu alaka