Buhari bai taba cin amana ba- El Rufai
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Babu wanda zai iya ja da Buhari a zaben 2019 – El-Rufai #BBCNigeria2019

  • Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da gwamnan.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa'i ya ce ba a taba dan siyasa ko ma'aikacin gwamnati da talakawa suka yarda da shi a kasar kamar Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya ce 'yan kasar sun san tarihin shugaban bai taba cin amana a ayyukan da ya gudanar ba a baya.

Ya bayyana haka ne da wata hirar musamman da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce babu wani dan siyasa da zai iya kayar da Shugaba Buhari.

Ya kuma soki tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, inda ya ce "idan aka ji Obasanjo na maganganu akwai abin da ya nema a gwamnati bai samu ba. Saboda haka ba don Allah yake yi ba," in ji Gwamna el-Rufai.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu akwai abubuwan da ya kamata a kara gyarawa a gwamnatin Buhari.

Amma ba zai bayyana su ba, saboda a cewarsa ba ya ba da shawara a kafafen yada labarai. Ya ce idan zai ba shugaban shawara zai kebe ne da shi a fadarsa.

Har ila yau ya bayyana daukar Dokta Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2019 a matsayin wani yunkuri na ci gaban jihar, ba wai don kawo rabuwar kai a bangaren addini ba.

A bangaren korar malamai ya bayyana cewa mafi yawancin malaman da aka korar a jihar "jahilai ne saboda bai kamata a ce suna aji suna koyarwa ba," in ji ta.