Akwai yiwuwar a ci Facebook tara

Facebook Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin sada zumunta da muhawara na Facebook,ya samu ribar kusan dala biliyan tara a watannin hudun karshen shekara ta 2018.

Kamfanin da ribarsa ta kai dala biliyan 22 a tsawon shekarar da ta gabata, ya samu habbaka da kaso 39 sama da shekara ta 2017.

Wannan dai na nuna cewa kamfanin bai samu gibi ko akasin haka ba, duk da irin badakalar da ya sha fama da ita a shekarar da ta gabata kan kare hakkokin bayanan sirri.

Duk da cewa masana na ganin kamar masu amfani da shafin na nuna halin ko'in kula a kan irin wadannan badakala, hukumomin da alhakin sanya ido ke kansu ba za su yi kasa a gwiwa ba, kuma mai yi wuwa ne nan bada jimawa ba a ci kamfanin tara mai dimbin yawa.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka