Saudiyya 'ta kammala yaki da cin hanci da rashawa'

An kama yarimomi da ministoci da 'yan kasuwa fiye da 200 kuma an tsare akasarinsu a otal-otal da ke, Riyadh, ciki har da otal din alfarma na Ritz-Carlton. Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption An kama yarimomi da ministoci da 'yan kasuwa fiye da 200 kuma an tsare akasarinsu a otal-otal da ke, Riyadh, ciki har da otal din alfarma na Ritz-Carlton.

Gwamnatin Saudiyya ta ce ta kawo karshen shirinta na kakkabe cin hanci da rashawa wanda ta kaddamar a 2017, lamarin da ya aka kama daruruwan yarimomi da attajirai.

An kwace kaddarori na fiye da $100bn - cikinsu har da kudi da gidaje - daga wurin wadannan mutane, in ji jami'an gwamnatin kasar.

Sun kara da cewa an kulla yarjejeniya da mutum 87 wadanda suka amince da tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Mutum takwas sun ki amincewa da wadannan zarge-zarge inda aka mika su ga masu shigar da kara.

Kazalika ba a cimma matsaya a kan zarge-zarge 56 ba saboda har yanzu ba a bincike a kansu ba.

A watan Nuwamba na 2017 ne Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya bayar da umarnin kaddamar da shirin.

An kama yarimomi da ministoci da 'yan kasuwa fiye da 200 kuma an tsare akasarinsu a otal-otal da ke, Riyadh, ciki har da otal din alfarma na Ritz-Carlton.

Kamun da aka yi wa mutanen ya zo wa 'yan kasar da matukar ba-zata wadanda suka yi matukar mamaki, a cewar editan BBC a kasashen larabawa Sebastian Usher.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption Yarima Mohammed bin Salman ne ya kaddamar da shirin

Labarai masu alaka