Zan kwace kudin masu rashawa, na yi musu afuwa - Atiku

Atiku Hakkin mallakar hoto Twitter/@NTA
Image caption Atiku ya ce ba a taba fuskantar matsalar tsaro kamar wannan lokaci ba

Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce idan ya zama shugaban kasa zai kwace kudi daga wurin mutanen da aka samu da laifin cin hanci da rashawa sanna ya yi musu afuwa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da shi da mataimakinsa Peter Obi suke amsa tambayoyi daga wurin fitacciyar 'yar jaridar na Kadaria Ahmed ranar Laraba da almuru.

Atiku Abubakar ya ce hakan zai fi zama mafi muhimmanci a yaki da rashawa da cin hanci maimakon a kai mutanen kotu abin da ka iya kawo jan-kafa wurin shari'a.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce irin wannan tsari ne kasar Turkiyya take bi, yana mai cewa hakan zai fi kyau a madadin dabarar da masu cin hanci suka bullo da ita ta shiga jam'iyya mai mulki sannan a kyale su ba tare da an hukunta su ba.

Dan takarar na jam'iyyar PDP ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi masa na hannu a cin hanci da rashawa, yana mai kalubalantar duk wanda yake da shaida a kan hakan da ya kai shi kotu.

Ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda take ikirari inda ya kara da cewa shi ne mutum na farko da ya assasa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC.

"Lokacin da aka kafa EFCC a 2004 ba su da kudin da za su soma aiki; ni ne na karbi N300m daga wurin hukumar da ke sayar da kaddarorin gwamnati na ranta musu. Daga bisani da aka yi kasafin kudi suka mayar da kudin."

Atiku Abubakar ya ce ba a taba samun matsalar tsawo a Najeriya kamar wannan lokaci ba.

A cewarsa "A baya yankin arewa maso gabas ne kawai ke fama da matsalar tsaro, amma yanzu dukkan arewacin Najeriya na cikin matsalar tsaro. Ku duba abin da ke faruwa a arewa ta tsakiya da arewa maso yamma, babu zaman lafiya."