'Kwankwaso ba zai sa in yi abin da zai cutar da Kano ba'

Abba Kabir Yusuf
Image caption Abba Kabir Yusuf

Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya ce ya tabbatar tsohon gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso ba zai sa ya yi abin da ba daidai ba.

Da aka tambaye shi, shin idan Kwankwaso ya bukaci ya yi abin da ya saba wa manufofin ci gaban Kano zai bijire masa? Sai ya ce ba bijirewa zai yi ba, zai yi kokarin ganar da shi gaskiya ne ta hanyar bayani.

"Na san halin Kwankwaso tamkar yadda na san yunwar cikina, ina da tabbaci ba zai sa na yi abin da ya sha bamban da ci gaban Kano ba", a cewar Abba.

An yi wa Abba tambayar ne a lokacin muhawarar 'yan takarar gwamnan jihar Kano da ta gudana ranar Asabar din da ta gabata.

Wani daga cikin mutanen da suka halarci muhawarar ne ya yi wa dan takarar tambayar ko ta wace hanya zai bi wajen gujewa irin matsalar da ta faru tsakanin Kwankaso da Ganduje ganin cewa Kwankwaso ya taka rawa wurin samun nasarar Ganduje ga shi kuma ya daga hannun Abba a yanzu?

Abba ya amsa da cewa " kowa da halinsa, wani yana da rike amana wani yana cin amana, wani kuma ba zai iya nuna maka cewa zai ci amanar ka ba."

"Munga illar cin amana, mun ga illa ta mutum ka taimake shi ka zama sila shi kuma ya zamo shine makiyinka."

Ya kuma ce "Da a ce an aikata alheri an yi biyayya da yanzu ana nan wurin sai an riga mu zuwa."