Fafaroma Francis zai ziyarci Abu Dhabi a karon farko

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hadaddiyar Daular Larabawa na da mabiya darikar Katolika miliyan daya

A karon farko, Fafaroma Francis zai ziyarci Hadaddiyar Daular Larabawa a yau Lahadi, ziyara irinta ta farko a tarihi da wani Fafaraoma ya taba kai wa yankin.

Fafroman zai kai wannan ziyara ce bayan da Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Sheikh Mohammed bin Zayed al-Nahyan ya mika masa goron gayyata domin ya halarci wani taron sasantawa tsakanin mabiya addinai daban daban a kasar.

Ana sa ran mutum 120,000 za su halarci wani taron ibada na mabiya darikar Katolika a yayin wannan ziyarar da zai kai kasar.

Masu nazarin siyasar yankin za su sa ido su ga ko Fafaroman zai ambaci yakin da ake gwambzawa a makwabciyar kasar Yemen.

Fafaroman dai ya yi kakkausar suka ga yadda ake gudanar da yakin, wanda Hadaddiyar Daular Larabawa ta shiga ciki tsundum a karkashin jagorancin Saudiyya.

A bara ya yi kira ga kasashen duniya da su "guji daukan matakan da ka iya sake dulmiya Yemen cikin rikici".

Hadaddiyar Daular Larabawa na da mabiya darikar Katolika miliyan daya, wadanda yawancinsu 'yan asalin kasashen Philippines da Indiya ne.

A wani sakon bidiyo da Fafaroman ya fitar ranar Alhamis, ya ce "Ina farin cikin wannan dama da ubangiji ya bani domin rubuta wani sabon babi na dangantaka tsakanin addinanmu a kasarku mai albarka."

Ya yaba wa kasar, inda ya ce "kasa ce mai kokarin kawo daidaito wajen zamantakewar al'iumma, da 'yan uwantakar dan Adam da kumazama wata mahada ga mabanbantan al'adu da wayewar kawuna."

A yayin ziyarar, Fafaroman zai gana da Sheikh Ahmed al-Tayeb, wanda shi ne babban limamin masallacin al-Azhar na birnin al-Kahira na kasar Misar.

Wannan masallacin na daya daga cikin cibiyoyin nazarin addinin Musulunci musamman ga Musulmi 'yan Sunni.

Wakilin BBC na Sashin Larabci, Murad Batal Shishani wanda tuni ya isa Abu Dhabi, ya ruwaito cewa Fadar Vatikan za ta nemi a sassauta wa mabiya addinin Kirista hanin gina coci-coci, musamman ma a Saudiyya inda aka haramtawa mabiya addinan da ba Musulunci ba gina wuraren ibada.

Jami'an Vatikan sun ce suna bukatar a basu damar kafa ofisoshi a yankin domin kulawa da mabiya darikar Katolika da ke zama a yankin.

Labarai masu alaka