Gasar Komla Dumor ta 2019: BBC na neman 'yan jaridar Afirka masu tasowa

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
BBC na nema 'yan jaridar Afirka masu tasowa domin su fafata wajen lashe gasar Komla Dumor ta 2019.

BBC na nema 'yan jaridar Afirka masu tasowa domin su fafata wajen lashe gasar Komla Dumor, wacce ake kaddamarwa karo na biyar.

Ana gayyatar 'yan jarida daga nahiyar Afirka da su shiga gasar, wadda aka kirkire ta da nufin zakulo da kuma taimakawa 'yan jarida masu fasaha daga Afirka.

Wanda ya yi ko ta yi nasara za sushafe wata uku a hedikwatar BBC da ke London, don kara gogewa da sanin makamar aiki.

Za a rufe shiga gasar ranar 26 ga watan Fabarairu na 2019, da misalin karfe 11:59 na dare a agogon GMT.

An soma gasar ce domin tunawa da kuma girmama dan kasar Ghana Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a tashar labarai ta BBC, wanda ya yi mutuwar fuju'a a shekarar 2014, a lokacin yana da shekara 41 a duniya.

A wannan shekarar za a kaddamar da gasar ne a Lagos da ke Najeriya.

Bayan shafe wani lokaci da wanda ya yi nasara zai yi a London, zai/za ta kuma je wata kasa a Afirka domin yin labari a kan wani batu - za kuma a rarraba labarin ga kasashen Afirka da ma duniya baki daya.

Wadanda suka lashe gasar a baya:

  • 2015: Nancy Kacungira daga Uganda
  • 2016: Didi Akinyelure daga Najeriya
  • 2017: Amina Yuguda daga Najeriya
  • 2018: Waihiga Mwaura daga Kenya

Dan jaridar Kenya Waihiga Mwaura wanda ya yi nasara a gasar a bara ya rika aiko da rahotanni daga Togo kan muhimmin batu, wato yadda matasa ke amfani da shara wajen kirkirar mutum-mutumi na robot da kuma masamfura.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
An soma gasar ce domin tunawa da kuma girmama dan kasar Ghana Komla Dumor.

Waihiga zai kasance a wurin kaddamar da gasar ta 2019, inda zai jagoranci muhawarar da sashen BBC mai watsa shirye-shirye a kasashen duniya zai gabatar kan tasirin matasa a zaben Najeriya da ke tafe.

Da yake jawabi kan gasar ta bana, daraktan yada labarai na BBC, Jamie Angus, ya ce: "A wannan zamani da ba a bai wa aikin jarida na hakika muhimmanci ba, yana da kyau mu yi duba ga 'yan jaridar da suka fahimci irin labaran Afirka da za su aike wa duniya ta yadda za a san abubuwan da ke faruwa a nahiyar."

"Dukkan wadanda suka lashe gasar a baya sun nuna cewa su 'yan jarida ne masu hazaka, kuma sun gabatar da hanyoyin da za a yi mu'amala da masu saurarenmu da ke karkara. Muna farin cikin ci gaba da gudanar da wannan gasa ta Komla da fatan za mu sake samun wani ko wata fitaccen dan jaridar da zai yi nasara daga nahiyar."

  • Domin sanin ko kun cancanta ku shiga gasar, latsa nan, click here
  • Za kuma ku iya aika wannan sako ta kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da #BBCKomlaAwards.

Labarai masu alaka