Yadda za mu bunkasa kasuwanci a Kano – 'Yan takarar gwamna

Yadda za mu bunkasa kasuwanci a Kano – 'Yan takarar gwamna
  • Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

'Yan takarar gwamna hudu da suka halarci muhawarar da BBC ta shirya a Kano sun bayyana yadda za su bunkasa harkokin kasuwanci a jihar, idan suka samu nasarar zama gwamna.

'Yan takarar sun hada da Mustapha Getso na jam'iyyar NPM, da Salihu Sagir Takai na jam'iyyar PRP da Maimuna Muhammad ta jam'iyyar UPP da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP.