Ko 'yan Najeriya za su yi 'sak' a zaben 2019?

Masu zabe kan kafa dogayen layuka yayin tantancewa da kuma kada kuri'a Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Najeriya da dama sun dawo daga rakiyar sak

Ga alama zaben 2019 a Najeriya zai banbamta da na 2015 musamman wajen zaben 'yan takara.

A zaben 2015 wasu 'yan Najeriya sun bi wani tsarin wata jam'iyyar siyasa da ake kira 'Sak' wajen zaben 'yan takara ba tare da la'akari da cancanta ba.

Amma yanzu ana ganin mutane sun kara wayewa na bin tsarin jam'iyya bayan sun dandani tsarin 'Sak.'

Wayewar da mutane suka yi, ake ganin wasu kananan jam'iyyu a Najeriya za su iya yin nasara a wasu kujeru na 'yan majalisar tarayya da na jihohi a zaben 2019.

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabambanta kan 'sak' a babban zaben 2019.

Yayin da wasu suka ce har yanzu suna kan tsarin, wasu kuma watsi suka yi da shi.

Ma'anar 'Sak'

'Sak' wata kalma ce da aka kirkira a siyasar Najeriya a lokacin zabe.

'Yan siyasa da magoya bayansu na amfani da kalmar Sak domin nuna cikakken goyon bayansu ga jam'iyyar da suke mara wa baya.

Kuma kalmar a siyasance tana nufin jefa wa 'yan takarar jam'iyya daya kuri'a tun daga zaben kansila har zuwa matakin zaben shugaban kasa.

Tushen 'sak'

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masana dai na ganin tun a 2003 kalmar 'sak' ta samo asali.

Masanin siyasa a Najeriya Malam Kabiru Sufi na kwalejin share fagen shiga jam'ia ta jihar Kano ya ce, 'sak' dai ta samo asali ne tun gabanin zaben shekarar 2003 yayin ziyarar yakin neman zabe da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar Kano, lokacin yana takarar shugabancin kasa a jam'iyyar ANPP.

"Yayin da Buhari ya yi kokarin daga hannun Malam Ibrahim Shekarau dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyarsu ta ANPP sai wasu daga cikin magoya baya suka rika kiran sunan wani dan takarar daban", in ji shi.

Wasu Rahotanni sun nuna cewa sunan Umar Yakubu Dan Hassan dan takarar gwamna na PSP ne ake kira a lokacin saboda farin jininsa a jihar.

Ganin haka sai Muhammadu Buhari ya ce to a zabi "ANPP sak", wato a zabi jam'iyyarsu a kowanne mataki.

Daga nan ne kalmar 'sak' ta zama ruwan dare a bakin 'yan siyasa da magoya bayansu.

Sai dai Malam Kabiru Sufi ya ce a yanzu kalmar na nufin jefa wa wata jam'iyya kuri'a a kowanne mataki ba lallai sai ta Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Tasirin 'sak'

Kabiru Sufi ya ce tasirin 'sak' ya bai wa wadansu 'yan siyasa da dama nasara a zabuka.

"Sak ta sa 'yan siyasa da dama sun ci zabe wandanda ba lallai ne su iya yin nasara ba."

"Talakawa ba sa wani amfana da 'sak', 'yan siyasa ne kawai suke amfani da ita don cimma bukatunsu na siyasa," in ji shi.

Shin Buhari yanzu yana 'sak'?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsarin siyasar Sak ya yi tasiri a 2015

Ana ganin shugaba Buhari da ya kirkiri kalmar Sak a siyasar Najeriya yanzu ya sauya ra'ayinsa.

A wata hira da ya yi da wata kafar yada labarai a 2018 Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci 'yan Najeriya da kada su zabi gwamnonin da suka gaza biyan albashin ma'aikatan jihohinsu.

Bincike kuma ya nuna cewa cikin gwamnonin da suka gaza biyan albashin har da na jam'iyyarsa ta APC.

Ko za a yi 'sak' a 2019?

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabambanta kan ko za su rungumi siyasar 'sak' a zaben 2019.

"Masu zabe da dama na cewa idan ka yi sak za ka ga sak, ko kuma wake da shinkafa za su yi, Kuma hakan ba ya rasa nasaba da yadda wasu 'yan siyasar suka kasa tabuka komai a mulkinsu", in ji Kabiru Sufi.

Ya kuma ce yanayin da talakawa suka tsinci kansu a yanzu shi ne zai sa su ki yin 'sak' din, kuma hakan ya dace da ra'ayoyin wasu ma'abota shafin Facebook na BBC:

Image caption Ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya
Image caption Ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya

Yayin da wasu ke cewa sun yi watsi da salon tsarin sak wasu kuwa cewa suke za su yi, domin a cewarsu bara-gurbi sun fita daga jam'iyyarsu:

Image caption Ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya

Wasu kuwa 'sak' din za su yi amma mai canji:

Image caption Ra'ayin wani dan Najeriya