Kungiyar malaman jami'oi ta Najeriya ta dakatar da yajin aiki

ASUU Hakkin mallakar hoto @BREAKINGNEWSNIG

Kungiyar malaman jami'oi ta kasa a Najeriya ta dakatar da yajin aikin watanni uku da ta shafe ta na yi.

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan cimma yarjejeniya da ta ce ta yi da gwamnatin kasar kan bukatunta.

Farfesa Muhammad Muttaka Usman, ma'ajin kungiyar ta ASUU, kuma malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya shaida wa BBC cewa, bayan tattaunawa da dama da kungiyar ta sha yi da gwamnati, yanzu gwamnatin ta amince da biya musu bukatunsu.

Farfesan ya ce, yarjejeniyar da suka cimma a yanzu ta wucin gadi ce, saboda nan bada jimawa ba za su koma su ci gaba da tattaunawa a kan gundarin yarjejeniyar 2009 wadda za a fara a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2019.

Ya ce, yanzu gwamnati ta yi wasu abubuwa ne, amma za a koma ne domin a dubi abubuwan da yarjejeniyar 2009 ta kunsa sai a tattauna a kansu aga me gwamnati za ta iya yi da kuma wanda ba za ta iya ba, sai su san mataki na gaba.

Farfesa Muhammad Muttaka Usman, ya ce zuwa Litinin 11 ga watan Fabrairu 2019, kowa a karkashin kungiyar zao koma bakin aiki, sannan kuma za a bude jami'oi na kasa.

Ita dai kungiyar ta ASUU, ta jima tana kai ruwa rana da gwamnati a kan bukatunta na neman a inganta yanayin aiki da kuma jami'oin abinda sau da dama ke haifar da yajin aikin wanda ake ganin yana matukar rage ingancin karatu a jami'oin kasar.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki bayan kasa fahimtar juna tsakaninta da ministan ilimi Adamu Adamu kan bukatunta.

Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami'o'in, da kuma rashin biyan mambobinta kudaden alawus da wasu sauran bukatunta.

Dakatar da yajin aiki ya zo ne kusan mako guda kafin zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019.

Labarai masu alaka