'Dole a yi wa 'yan majalisa maza kaciya'

Kaciyar maza Hakkin mallakar hoto AFP

Wata 'yar majalisa a Tanzania ta yi kiran da a duba kowanne dan majalisa a kasar domin gano wadanda ba a yi wa kaciya ba.

Jackline Ngonyani, ta ce duk dan majalisar da aka gano cewa ba a yi masa kaciya ba, to yakamata ya je ayi masa saboda a cewarta hakan zai rage hadarin yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki.

Wannan ra'ayi na 'yar majalisar, ya janyo rabuwar kawuna a zauren majalisar.

Ana dai kallon cuta mai karya garkuwar jiki a matsayin babbar barazanar ga lafiyar al'umma a kasar Tanzania.

An dai yi wa kusan kaso 70 cikin 100 na mazan kasar kaciya.

An yi amanna cewa, kusan kaso biyar cikin 100 na mazan da suka manyanta a kasar sun kamu da cuta mai karya garkuwar jiki, lamarin da ya shigar da kasar ta zamo ta 13 a duniya a yawan masu wannan cuta.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce yin kaciya na rage hadarin sha'awar saduwa ga maza barkatai.

Yawancin kasashen Afirkan da ke yaki da cutar HIV, sun kaddamar da gangamin karfafa gwiwar maza a kan su yi kaciya.

'Yar majalisar, ta bayar da wannan shawarar ce a yayin wata muhawara da aka yi a zauren majalisar a kan yadda za a shawo kan yaduwar cutar HIV a kasar.

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun goyi bayan shawarar ta ta, yayin da wasu kuma suka soki shawarar.

A makwabciyar kasar ta Tanzania wato Kenya, wasu manyan 'yan siyasa a kasar sun yi sun bigi kirji sun je an yi musu kaciya a shekarar 2008, domin bayar da misali da kuma karfafa wa maza gwiwa a kan su je ayi musu kaciyar idan ba a taba yi musu ba.

Labarai masu alaka