Buhari ya hana Atiku wurin taro a Abuja - PDP

Dan takarar PDP Atiku Abubakar Hakkin mallakar hoto Getty Images

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi Buhari da jam'iyyarsa ta APC da hana dan takararta Atiku Abubakar filin taron yakin neman zabensa a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin jam'iyyar Kola Ologbondiyan ya raba wa manema labarai, ta ce an hana su filin taro na Old Parade Ground a birnin Abuja, duk da sun riga sun biya kuma sun samu izinin amfani da filin taron.

PDP ta shirya gudanar gangamin siyasar ne a ranar Asabar a ci gaba da yakin neman zaben dan takararta Atiku Abubakar.

Zuwa yanzu babu martani da ya fito daga fadar shugaban kasa ko daga jam'iyyar APC mai mulki kan dalilin hana dan takarar na PDP gudanar da gangamin yakin neman zabensa a Abuja.

APC mai mulki tana gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa a Lagos a ranar Asabar, yayin da PDP ta shirya yin gangaminta a Abuja.

A cikin sanarwar, PDP ta ce tun da farko ta shirya gudanar da taron siyasarta ne ranar Asabar a Lagos amma saboda ya ci karo da na APC ta yanke shawarar gudanar da nata a Abuja.

Ta ce tana fatan gwamnatin APC za ta bari ta gudanar da gangamin da ta dage zuwa Talata a birnin na Lagos.

Babbar jam'iyyar ta adawa ta gode da kuma ba magoya bayanta hakuri wadanda tuni suka iso Abuja domin taron.

Yakin neman zaben 'yan takarar manyan jam'iyyun biyu na ci gaba daukar hankali, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka sanya wa hannu da ta kunshi kaucewa rikici a lokacin yakin neman zabe da tabbatar da an yi zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.