Abubuwa biyar game da muhawarar Sokoto

Muhawarar Sokoto

'Yan takara biyar da ke neman gwamna a jihar Sokoto sun tafka muhawara da BBC Hausa ta jagoranta.

'Yan takarar sun hada da Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP da Aliyah Sa'idu Kebe ta jam'iyyar KOWA Party da Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC da Abba Sidi na jam'iyyar NCP sai kuma Muhammad Sadiq Abubakar na jam'iyyar SDP.

Wannan ce muhawara ta karshe a jerin muhawarorin da suka gudana bayan an fara da Nasarawa da Gombe daKano sai kuma a karshe a Sokoto.

Ga wasu daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a wannan muhawarar:

Zan magance talauci ta hanyar rokon Allah - Aliyah

Aliyah ta ce za ta magance talauci ne ta hanyar rokon Allah sannan za ta gayyaci masu ba da agaji daga waje.

Ta ce idan mata sun fito takara ana cewa ba su da ilimi da tarbiya, tana mai cewa hakan bai dace ba.

Zan kori malamai - Sadiq na SDP

Abubakar Sadik na SDP ya ce zai rage malamai maras inganci idan har ya zama gwamnan jihar Sokoto.

Ya ce a matsayinsa na dan kasuwa, cikin shekara biyu zai daina dogaro da kudin gwamnatin tarayya.

Dalilin da ya sa na rabu da Tambuwal - Ahmed

Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC ya ce ya sauka daga mukaminsa na mataimakin gwamnan Sokoto saboda gwamnati ba ta yin ayyukan da suka dace.

Kuma wannan ne dalilin da ya sa ya fito takarar gwamna domin kada gwamna Tambuwal.

Muhawarar ta ja hankali ganin yadda 'yan takarar biyu suka hadu.

Sokoto ta fi Kebbi a harakar noma - Tambuwal

Tambuwal na PDP ya ce abin da ya sa ba a ganin aikin da yake yi shi ne "saboda dokin mai baki ya fi gudu".

Ya ce jiharsa ta fi Kebbi bayar da muhimmanci kan noma, ita kuwa Zamfara rashin tsaro ya sa ko gonar ba a iya zuwa.

Ya shugaban kasa da kan Muhammadu Buhari ya jinjina wa gwamnatinsa kan yadda ta bunkasa harakar noma.

Zan samar da ilimi ga kowa - Sidi

Abba Sidi na NCP ya ce zai tabbatar da kowa ya samu ilimi a Sokoto.

Zai bunkasa kiwon lafiyar yara da tsoffi da mata.

Ya ce zai inganta kasuwanci da raya kasa.