Gangamin Zabe
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zaben 2019: Shin taron jama'a ne cin zabe a Najeriya?

Latsa alamar lasifika a sama domin sauraren sharhin Dakta Abubakar Kari

Ganin cewa manyan zabuka na karatowa a Najeriya, 'yan takara tun daga matakin majalisar jiha har zuwa na shugaban kasa na ta kai komo domin gudanar da taruka.

A lokacin gangamin yakin neman zabe, akan samu katafaren fili, inda 'yan takara da masu ruwa da tsaki a jam'iyya kan hau mumbari domin bayyana manufofinsu.

Wasu na ganin cewa yawan jama'a da ake tarawa a wurin gangamin yakin neman zabe, na nuna karbuwa ko rashin karbuwar dan takara ga masu zabe.

Sai dai masharhanta siyasa na ganin jama'a da suke hallartar gangami ko yakin neman zabe ba lallai su kasance manuniya ga nasara ko rashin nasara da dan takara zai iya samu ba.

Dakta Abubakar Kari, malamin kimiyyar siyasa a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa kiyasi ya nuna da dama cikin masu hallartar irin wannan gangamin yakin neman zabe a Najeriya ba su da katin zabe, kuma ko suna da shi yawancin su ba su fitowa ranar zaben.

Da aka tambayi Dakta Kari ko yawan taron jama'a yana tasiri a zukatan masu zabe wajen sauya ra'ayinsu?

Sai ya ce "ba na tsammanin haka, bincike ya nuna cewa a Najeriya yawancin mutane sukan yanke hukuncin wa za su zaba watanni kafin zaben ya zo."

"Musamman a wannan zamani na amfani da shafukan sada zumunta na intanet, 'yan jam'iyya daban-daban kan yi amfani da shafukan domin watsa hotuna na gangami da 'yan jam'iyyar tasu ta gudanar a matakai daban- daban domin nuna nasarar su," in ji shi.