'Gwamnati ki cika alkawarin ceto 'ya ta Leah'

Makarantar Dafchi Hakkin mallakar hoto Reuters

Mahaifiyar yarinyar nan daya tilo da mayakan Boko Haram ke rike da ita daga cikin 'yan matan makarantar Dafchi da suka kama kuma suka ki saki, wato Leah Sharibu, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta cika alkawarin da ta yi na cewa za ta ceto 'yar tasu daga hannun kungiyar ta Boko Haram.

Mahaifiyar cikin sassanyar murya da kuma sheshshekar kuka, ta ce kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi alkawarin ceto musu 'yar su, yakamata a duba.

Ta ce, har ministoci uku gwamnatin tarayya ta tura musu gida a kan su tabbatar mata da cewa za a ceto mata 'yarta, amma har yanzu ba ta ga Leah ba.

Mahaifiyar Leah ta ce, a ranar 19 ga watan Fabrairu mai zuwa ne, Leah za ta cika shekara guda a hannun 'yan Boko Haram.

Ta ce ganin cewa har gashi 'yarta za ta cika shekara guda da sacewa kuma ta ji shiru, shi ya sa ta ke sake tuna wa gwamnati a kan kada a manta da 'yarta Leah.

Mahaifiyar Leah ta ce ' Leah yarinya ce tana shekara 14 aka sace ta a wajen wadanda suka saceta ta cika shekara 15'.

Ta ce ' Yakamata gwamnati ta duba ta taimakeni ta ceto mini 'ya ta domin kowa ya san dadin yaro, ku saka kan ku a matsayina, idan da ku ne ya zaku ji?''

A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan makarantar sakandiren Dafchi da ke jihar Yobe.

Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi ciki har da Leah, kuma an sace su kwana daya bayan sojoji sun fice.

An dai shiga rudani a kan sace 'yan matan, kuma sai da aka dauki tsawon mako guda kafin gwamnati ta amince an sace su.

Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan.

Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok

Labarai masu alaka