Facebook zai mayar da hankali kan harshen Hausa

A yanzu akwai Hausa da harsunan Afirka 27 a shafin na Facebook Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A yanzu akwai Hausa da harsunan Afirka 27 a shafin na Facebook

Shafin Facebook ya bayyana cewa za ya dauki ma'aikata sama da 100 domin mayar da hankali kan rubuce-rubucen da ake yi a shafin a harshen Hausa da wasu guda uku na Afirka.

Wannan na zuwa ne bayan da wani bincike da BBC tayi wanda ya nuna gazawar Facebook a kan magance yada labaran karya da maganganun kiyayya a shafin.

Kuma binciken ya nuna cewa Facebook tare da hadin gwiwar wani kamfani da ke taya su tantance rubutu a harsunan Afirka na da mutane hudu kacal dake bitar rubuce-rubucen da ake yi.

A shekarar da ta gabata, kasashe da dama sun sanya dokoki da suka shafi shafukan sada zumunta kuma harda Facebook a cikinsu.

Wani kwamiti na majalisar dattawa a Amurka ya gayyaci shugaban kamfanin inda kwamitin ya nemi ya amsa tambayoyin.

A farkon wannan shekarar ne Facebook ya bayyana aiwatar da wasu sabbin tsare-stare domin magance katsalandan a zabuka a kasashen Najeriya, Ukraine da India.

Kamfanin ya bayyana cewa a kullum yana koyon abubuwa da dama daga jama'a kuma yana kokarin inganta shafin.

Labarai masu alaka