Zaben Najeriya 2019: Kalubale tara da Najeriya ke fuskanta

Tutar Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images

BBC ta yi nazari a kan kalubalen da Najeriya ke fuskanta a matsayin kasar da ta fi kowace yawan jama'a da karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Wannan nazarin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar zaben shugaban kasa shekaru 20 bayan dawo wa kan mulkin dimokuradiya.

Shekaru hudu da suka gabata, Shugaban kasar Muhammadu Buhari na jami'yyar APC ya samu goyon bayan arewa da kuma kudu maso yammacin kasar, inda kuma babbar jam'iyyar adawa a kasar watau PDP ta fi karfi ne a kudanci da kuma kudu maso gabashin kasar.

Amma ba kamar a 2015 ba inda aka samu shugaba Muhammadu Buhari daga arewa ya fafata da dan kudu watau shugaban kasar wancan lokaci Goodluck Jonathan.

Amma a wannan karon, dukkanin 'yan takarar sun fito ne daga yankin arewa wato shugaba Buhari da tohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Masu sharhi na cewa wannan zaben na da wuyar hasashe musamman ta bangaren wanda zai lashe zaben.

Jam'iyyar APC za ta iya shan wahala a jihohin yankin tsakiya kamar su Benue da Nasarawa sakamakon rashin jin dadin da ake nunawa na kin magance rikicin kabilanci kamar yadda daya daga cikin editocin BBC a Najeriyar Aliyu Tanko ya bayyana.

Jami'iyyar APC ta yi suna a jihohin Legas da Kano kuma sune jihohin da suka fi yawan masu jefa kuri'a amma kalubalen da za a iya fuskanta shi ne nuna halin ko in kula da karancin fitowar mutane da za a iya samu wajen jefa kuri'a.

Wannan taswirar ta nuna karfin tattalin arzikin yankunan Najeriya.

Taswirar ta nuna kudancin kasar ne kan gaba fiye da arewacin Najeriya.

Jihar Katsina ce jihar da shugaban kasar ya fito kuma ta fi zama koma-baya inda aka kwatanta matsakaicin mutum na samun kasa da dala 400 a shekara kwatankwacin dala daya ke nan a rana.

A dayan bangaren kuma babban birinin tarayyar kasar Abuja da kuma jihar Legas sune suka fi karfin tattalin arziki da bunkasar kasuwanci inda matsaikaicin mutum ke samun kusan dala 800 a shekara.

Jihohin Delta da Bayelsa da Ribas da Akwa Ibom da ke kudancin kasar suna samun arziki ne sakamakon harkar man fetur.

Wadannan alkaluma na nuna adadin kwatankwacin kudin da matsakaicin mutum ke samu ne ba wai yadda ake raba kudade a yankuna daban-daban na kasar ba.

A duk shekara, dubban matasa 'yan Najeriya ne ke neman ayyukan yi amma kadan daga cikinsu ne ke samun damar samun aikin.

Samun wadatattaun ayyukan yi na daga cikin kalubalen da Najeriya ke fuskanta kamar yadda wani kamfani na Pwc ya bayyana a bara.

Amma duk da matsalolin da kasar ke fuskanta, tattalin arzikin kasar ya karu sossai tun daga shekarar 2000 amma rashin aikin yi na ci gaba da zama matsala inda yake karuwa a kullum.

A yanzu haka rashin aikin yi a kasar ya kai kusan kashi 23 cikin 100.

Amma abin mamaki shi ne wasu daga cikin jihohin da ke da arzikin man fetur suna fama da matsalar rashin aikin yi.

Wannan na nufin kamfanonin man fetur a yankin ba su samar da wadatattun ayyukan yi ba.

Kamfanonin man fetur da iskar gas suna cikin kashi tara cikin 100 na ma'aunin tattalin arzikin Najeriya na GDP, amma kudaden da kasar ke samu ta wannan bangaren na karewa ne ta bangaren hidimomin gudanar da gwamnati.

Farashin man fetur a kasuwannin duniya na taka muhimiyyar rawa wajen sanin ko gwamnati na iya biyan bassusukanta.

Farkon wa'adin mulkin Shugaba Buhari ya ci karo ne da karewar farashin man fetur wanda hakan ya janyo tashin gwauron zabbi da bassusukan kasar suka yi.

Matsalar tsaro a lokacin zabe na jawo matsala inda ake samun arangama tsakanin kabilu da kuma kungiyoyin da ke ikirarin jihadi wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum 10,000 a shekaru hudu da suka wuce.

Duk da nasarori da jami'an soji suka samu tun a 2015 musamman wajen kwato yankunan da 'yan kungiyar Boko Haram suka mallaka a arewa maso gabashin kasar, a yanzu haka ana ci gaba da samun hare-hare daga kungiyar.

A arewa maso yammacin kasar musamman jihar Zamfara, rashin tsaro na kara tabarbarewa inda barayi ke kai hari a kauyuka suna kashewa tare da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma satar shanu.

Wannan daddaden rikicin da ya shafi manoma da makiyaya ya kara tabarbarewa ne a 'yan shekarun da suka gabata musamman a arewa maso tsakiyar kasar.

Ana dai caccakar gwamnatin Buhari sakamakon rashin daukar kwararan matakai wajen shawo kan wannan matsalar amma lamarin ya dan lafa a daidai lokacin da zabe ke karatowa a kasar.

Yawan mutanen Najeriya da suka kai mutum miliyan 180 sun rabu ne yaruka daban-daban.

Al'ummar Hausa-Fulani wadanda suka mamaye arewacin kasar akasarin su Musulmai ne.

Bangaren kabiliyan Yoruba da suka watsu a kudu maso yammacin kasar sun kasu ne Musulmai da Kirista.

Kabilar Igbo da ke kudu maso gabashin kasar da kuma makwabtansu akasarin su Kiristoci ne wasu kuma suna addinan gargajiya.

Duka 'yan takarar shugabancin kasar a yanzu watau Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar 'yan kabilar Fulani ne inda suke da mataimaka daga kudancin kasar.

Wanda Buhari ya zaba a matsayin mataimaki shi ne Yemi Osinbajo, dan kabilar Yoruba ne kuma fasto haka kuma farfesa ne a bangaren shari'a.

Shi kuma Atiku ya zabi Peter Obi ne matsayin mataimaki kuma dan siyasa ne daga yankin kabilar Igbo.

Kamar yadda asusun kananan yara na majalisar dinkin watau UNICEF ya bayyana, daya a cikin biyar na yaran da ba su zuwa makaranta a duniya daga Najeriya suke amma yawan yaran da ya kamata a ce suna zuwa makaranta ya bambanta a fadin kasar.

Akwai bambanci tsakanin yankunan inda aka samu gwargwadon yaran da ke zuwa makaranta daga arewa da ba su da yawa sosai.

An yi kiyasin cewa yara miliyan 10 da dubu dari biyar na yara daga 'yan shekara 4 zuwa 14 ba su zuwa makaranta.

A Okotban bara, wani jami'in Unicef din ya bayyana cewa kashi 65 cikin 100 na yaran sun fito ne daga arewacin Najeriya inda jihar Bauchi ce a kan gaba sai kuma garin shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Katsina.

Wata hukuma a kasar dai ta bayar da shawara a bara a kan cewa sai an kafa dokar ta-baci a bangaren ilimi domin shawo kan matsalar.

Yawan masu ilimi a arewa ya yi kasa musamman ga mata.