Wasu 'yan Najeriya sun bayar da shaida a kan kamfanin mai na Shell

Esther Kiobel
Image caption Esther Kiobel ta dade tana fafutukar ganin an yi mata adalci

Matar wani dan gwagwarmaya da ta maka kamfanin mai na Shell kara, kan zargin kashe mijinta, ta bayyana cewa mutuwarsa ta sanya ta cikin "rudani" da radadin talauci.

Esther Kiobel na bayar da shaida ne a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya dake Hague inda ta nemi a biya ta diyya.

Tana daga cikin mata hudu da ke zargin kamfanin da sa hannu wajen kisan da gwamnati ta yi wa mazajensu a 1995, duk da cewa kamfanin ya musanta zargin.

'Yan gwagwarmayar sun jagoranci zanga-zanga a kan kwararar mai a yankin Ogoni da ke yankin Naija Delta a Najeriya.

Gwamnatin soja a karkashin Janar Sani Abacha da kamfanin na Shell sun dauki zanga-zangar a matsayin barazana a garesu wanda hakan ya yi sanadiyyar rataye mutane tara tare da shugabansu, Ken Saro-Wiwa.

Hakkin mallakar hoto TIM LAMBON/GREENPEACE
Image caption Ken Saro-Wiwa shi ne jagoran masu zanga-zangar na Naija Delta a shekarun baya

Kasashen duniya da dama sun yi Allah-wadai da kisan, inda har kungiyar Commonwealth ta kori Najeriya daga cikinta.

Biyu daga cikin matan sun samu halartar zaman kotun a Hague, sauran kuma ba a ba su takardar izinin shiga kasar ba don haka ba su samu damar zuwa ba.

Me ya sa aka rataye masu fafutukar?

An rataye Saro-Wiwa da sauran masu fafutuka 8 ne bayan wani zaman sauraren kara na sirri da aka yi, wanda aka kama su da laifin kashe shugabannin gargajiyar yankin Ogoni 4.

Sun musanta zargin kuma sun ce sharri aka yi masu.

Firayim Ministan Birtaniya na wancan lokacin John Major ya bayyana shari'ar a matsayin "ta bogi."

A lokacin shari'ar, Saro-Wiwa ya ce an yi shirin hana mutanen Ogoni daga yaki da kwararar mai ne wanda ya lalata yankin sannan ya jefa al'ummar yankin cikin kangi na talauci da cuta.

Saro-Wiwa na daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar MOSOP, mai fafutukar kwato wa jama'ar Ogoni 'yancinsu.

Ya kaddamar da kamfe don samun diyya kan lalata muhalli da kuma neman a bai wa yankin kaso a cikin ribar man fetur.

Labarai masu alaka