Zaben 2019: Shin 'yan siyasa gaskiya suke fada kan tattalin arziki?

Wannan shi ne na uku cikin jerin bayanan da BBC ta shirya wanda ake fatan zai tabbatat 'yan takarar shugabancin Najeriya sun cika alkawurran da suka dauka.

Masu kada kuri'a a zaben shugaban kasa a Najeriya ran 16 ga Fabrairu za su yi zaben ne bisa abubuwan da 'yan takarar suka fada.

An tsara wannan shirin bin diddigi ne domin karkatar da yadda ake ruwaito bayanan zabe daga batutuwan siyasa zuwa ga batutuwan manufofi a Najeriya.

Amma ya za a yi su sani ko abubuwan da 'yan takarar suka fada masu gaskiya ne?

Bari mu bi mu gano.

Atiku Abubakar
Tambaya mafi muhimmanci a wannan zaben ita ce 'A yanzu, kun fi yadda ku ke shekara 4 da ta wuce?' Mun fi wadata ko mun fi talauci?
...
Tabbatar da gaskiya

Najeriya na ci gaba da zama kasa mai fama da tsananin talauci da rashin daidaiton a wajen rarrabuwar arziki. Atiku ya nuna cewa wadannan abubuwa basu sauya ba a shekaru 4 da suka gabata, watakila ma sun kara tabarbarewa.

Bayanai sun nuna cewa abun da ya fadi na iya zama dai-dai.

Gaba daya tattalin arzikin Najeriya, idan aka yi la'akari da arzikin kasar na cikin gida, ya na farfadowa daga matsin da ya shiga tun bayan faduwar farashin mai a 2016.

Tsakanin 2014 da 2017, kudin da 'yan Najeriya suka dogara da shi ya ragu daga dala 3,222 duk mutum daya a 2014 zuwa dala 1,968 duk mutum daya bayan shekara 3 kamar yadda gwajin Babban Bankin Duniya Ya nuna.

Haka kuma, gibin da ke tsakanin mafi arziki da mafi talauci cikin 'yan Najeriya na ci gaba da karuwa sosai.

Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka. Mujallar Forbes ta yi kiyasin cewa kudinsa ya kai dala biliyan 10.5.

Kusan rabin mutanen da ke kasar na rayuwa ne kasa da makin talauci da kasashen duniya suka amince da shi na dala 1.90 (Naira 133.5) kowace rana. Shekara 4 da ta wuce, 'yan Najeriya miliyan 85 ne aka ce suna fama da talauci, kuma wadannan alkalumma sun ci gaba da karuwa duk shekarar. A 2016, masu fama da talauci sun kai mutum miliyan 90, sannan a 2017 miliyan 94. A shekarar da ta gabata, Babban Bankin Duniya ya yi kiyasin cewa 'ayan Najeriya miliyan 97 ke rayuwa cikin talauci.

Matsanancin talauci a Najeriya na karuwa, inda kusan mutum 6 ke fadawa talauci duk minti daya ko kuma mutum miliyan 3.2 duk shekara. Hukumar Kididdigar Talauci ta Duniya ta yi kiyasin cewa 'yan Najeriya miliyan 120 ne za su fada talauci zuwa shekarar 2030.

Lamarin ya fi muni a arewacin Najeriya. Tsakanin 2004 da 2013, yawan mutanen da ke fama da talauci a kudancin kasar ya ragu da kusan miliyan 6, ya kuma karu a arewa da kusan miliyan 7.

A yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma, kawar da talauci ya cije kuma ya ci gaba da kasancewa da yawa- kashi 47.6 cikin dari da kuma kashi 59 cikin dari.

Rikicin Boko Haram ya shafi wasu sassan arewacin kasar kuma rashin samar da abubuwan more rayuwa daga gwamnati ya shafi yankunan.

Muhammadu Buhari
A bangaren noma, mun ga karuwar zuba hannayen jari a bangarori da dama. Kusan shekaru 3 da suka gabata, Najeriya na kashe dala miliyan 5 a rana kan shigo da shinkafa. A yanzu an daina shigo da shinkafa gaba daya. Lallai ne, mu na hanyar samun isasshen abinci kwanan nan.
Tabbatar da gaskiya

Shugaba Buhari ya yi kuskure.

Gwamnatin tarayya ta yi shirin zuba jari a fannin noma a shirinta na Farfado da Tattalin Arziki na 2017-2020.

Shirin dai na da burin tabbatar da cewa Najeriya tana noma shinkafar da za ta ciyar da duka 'yan kasar kafin 2018 da kuma alkama kafin 2020. Sai dai, ba a cika wannan burin na noman shinkafa kafin karshen shekarar da ta wuce ba, kuma cimma wa'adin iya noma alkama zai yi wuya.

Duk da cewa noman shinkafa a Najeriya ya karu a shekaru biyar din da suka gabata kuma ana sa rai zai karu a 2019, kasar na ci gaba da zama daya daga cikin kasashen da suka fi ko wanne shigo da shinkafa.

A shekarar 2014, farashin tan daya na shinkafa ya kama dala 425. A lokacin Najeriya na shigar da tan 2,600,000 na shinkafa wanda hakan ya kama gaba daya dala miliyan 3, 027, 400. Hakan ya kama kusan dala miliyan 3 duk rana, baya ga haraji.

A shekara ta 2018, farashin tan na shinkafa bai yi wani sauyi na a-zo-a-gani ba. Yawancin farashin na shinkafa a yanzu yana kusan dala 421 ne a kan kowane tan daya. Duk da raguwar shigar da shinkafar da aka samu zuwa cikin kasar, an shigar da shinkafar da ta kai ta tan 2,400,000 a shekara ta 2018, wanda duk da haka ana ganin kasar ta kashe dala miliyan biyu da 2,766,027.40, ko kuma dala miliyan 2.7.

Bukatar shinkafa ya karu tare da yawan mutanen kasar. har yanzu dai 'yan Najeriya ba su watsar da soyayyar da suke yi wa dafa-dukar shinkafa ba.

Rashin wadataccen abinci ya zama babbar matsala a Najeriya, kuma rikici a Arewa maso gabashi da yankin tsakiya ya shafi samuwar kayan abinci da kuma damar da iyalai ke da shi na samun abin sanyawa a bakin salati.

Tsarin da ke tantance adadin yunwa a kasashe da yankuna ya sa Najeriya a matsayin ta 103 cikin kasashe 119 a matakin yunwa kuma ana ganin wannan babbar matsala ce.

A watan Maris din 2018, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da Majalisar da ke kula da samar da isasshen abinci, wacce kuma majalisa ce da yake jagoranta domin samar da mafita a matsalar samar da isasshen abinci a Najeriya.

Kingsley Moghalu
Ana kashe sama da kashi 60 cikin dari na kudaden kasarmu kan biyan bashi inda ba a samun rara har a yi ayyukan ci gaba. Gwamnatina za ta dakatar da biyan basussukan da aka karba daga kasashen waje idan na hau mulki.
... 9 ga Disamba 2018 (Hira da Jaridar Punch)
Tabbatar da gaskiya

Alkalumman baya-bayan nan sun nuna cewa basussukan Najeriya sun karu daga Naira tiriliyan 7.55 (dala biliyan 24.66) a shekara ta 2012 zuwa Naira tiriliyan 22.43  (dala biliyan73.2) a shekara ta 2018, an samu karin kashi 196.9 cikin dari.

Domin kawar da wannan bashi gaba daya, kowane dan Najeriya zai biya Naira 118,046.33 (dala 385.33).

A shekarar 2017, gaba daya kudin da Najeriya ta samu ya kamna Naira tiriliyan 2.7 (dala biliyan 8.8) kuma an ware Naira tiriliyan 1.62 (dala biliyan 5.3) ga biyan bashi, wanda ya kama kusan kashi 59.68 cikin dari.

Wannan ba ya nufin cewa abin da Moghalu ya ce ba dai-dai ba ne, saboda akwai hanyoyi daba-daban na biyan bashin kasa. Babu yadda za a yi a sani ko Naira tiriliyan 1.62 (dala biliyan5.3) da aka ware domin biyan bashi ya fito ne daga gaba daya kudin da kasar ta samu.

Ana amfani da kason bashi da ma'aunin tattalin arziki na GDP wajen gwada yadda kasa ke saurin biyan basussukanta ta hanyar gwada adadin kudin da kasar ta karba bashi da karfin tattalin arzikinta. Idan kudin da ke cikin kasar ya fi bashin da ake bin kasar yaw, hakan na nufin kasar na da karfin tattalin arzikin biyan basussukanta. Idan bashin ya fi karfin tattalin arzikin kasar, hakan na nufin kasar za ta wahala wajen biyan bashinta.

A shekarar ta 2018, bashin da ake bin Najeriya ya fi karfin tattalin arzikinta da kashi 19.72 cikin dari, an samu kari daga 12.65 cikin dari a 2013.

Bashin waje shi ne kudin da kasashe da hukumomin waje ke bin kasar. Kusan kaso 29.49 cikin dari na bashin da ake bin Najeriya daga kasashen waje ne kuma Babban Bnakin Duniya ne ya fi ko wace hukuma bai wa Najeriya bashi.

A shekara ta 2017, an yi amfani da basussukan da aka karba daga waje, don yin ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da walwala da noma da samar da tituna.

A kasafin kudi na shekara ta 2019 an ware kusan kashi 25.65 cikin dari don biyan bashi.

Omoyele Sowore
Abin da nake nufi shi ne in ware dala biliyan 3.6 kuma za mu mayar da kasar nan kamar filin gini. Muna bukatar gidaje miliyan 17, sama da 'yan Najeriya miliyan 80 ne ba su da gidaje. Akwai bukatar mu tabbatar da cewa a kalla 'yan Najeriya biyar da na 'yancin samun gida: uba da uwa da a kalla 'ya'yansu 3.
Tabbatar da gaskiya

A 2012, ma'aikatar gidaje ta yi jimillar karancin gidaje a Najeriya wanda ya kama kusan gidaje miliyan 17 bisa ga alkalumman Babban Bankin Duniya. Gwamnati ta yi hasashen cewa zuwa shekara ta 2014, karancin gidaje zai kai gidaje miliyan 30 zuwa 40.

Sai dai Babban Bankin Duniya ya gano cewa mai yiwuwa an rage alkalumman da aka fitar a shekara ta 2012 saboda yadda Najeriya ta kiyasta  cewa za a samu mutum 6 a kowane gida, kuma hakan ya wuce yadda tsarin yake a sauran kasashen duniya inda ake da mutum 4.6 a kowane gida. Babban Bankin Duniya ya ce karancin gidajen ya tasar ma gidaje miliyan 30.

Tun shekara ta 2012, ba a sake samun wani bincike mai zurfi ba kan yawan gidajen da ake bukata a Najeriya don haka babu wanda ya san takamaimai yawan.

Ana yawan ambato gidaje miliyan 17 din da aka bayyana a baya amma ana mantawa da karuwar mutane a kasar da kuma rashin zuba hannayen jari don gina gidajen.

Abu ne mai wahala a iya kiyasta yawan mutanen da ba su da muhalli a Najeriya tunda rabon da ayi kidayar jama'a a kasar tun shekara ta 2006 kuma tashe-tashen hankula sun daidaita 'yan Najeriya da dama.

Sai dai a shekarar ta 2017, wata hukumar gwamnati ta yi kiyasin cewa 'yan Najeriya 108 ne ba su da muhalli.

Idan aka yi amfani da ma'aunin da ke nuna cewa 'yan Najeriya 5 ga gida guda da kuma mutane miliyan 108 da ba su da gidaje, karancin gidajen ya kai gidaje miliyan 26.

Dala biliyan 3.6 da Sowore ya bukata zai isa a gina gidaje 360,000 ne kawai.

Fela Durotoye
Idan muka gyara ayyukan noma, wanda a yanzu kusan kashi 60 cikin dari na ma'aikatan Najeriya na aiki ne a bangaren noma kuma kashi 35 cikin 100 kawai na kasarmu ake amfani da shi wajen noma. Za mu tabbatar da cewa ana mafani da kashi 50 cikin 100 na kasarmu wanda kuma hakan zai samar ma mutane miliyan 30 su samu ayyukan yi.
... 19 ga Janairu 2019 (Muhawarar 'yan takarar shugaban kasa)
Tabbatar da gaskiya

Yawancin mutanne da ke da aikin yi a Njeriya manoma ne. Kididdigar da Hukumar Kididdiga ta yi a rubu'i na 3 na shekara ta 2017, kashi 48.2 cikin 100 na ma'aikata na yin wani anu'i na noma kuma mafi yawansu na yin aikin noman sosai.

Kasuwanci, wanda shi ne bangare na biyu mafi girma da ke samar da ayyukan yi na smar da aiki ne ga kashi 14 cikin 100 na mutanen Najeriya, yayin da wasu bangarorin ke samar da ayyukan yi ga kashi 7.9 cikin 100 kuma bangaren masana'antu ke samar da ayyukan yi ga kashi 7.9 cikin 100 na 'yan kasar.

Fela Durotoye ya yi dai-dai wajen zayyano cewa yawancin ma'aikatan Najeriya na aiki ne a bangaren noma, sai dai kason bai kai yadda ya bayyana ba.

Mista Durotoye bai kauce hanya ba da ya ce ana amfani da kashi 35 cikin 100 na kasar noma.

Kashi 37 cikin dari na kasar noman Najeriya ne kawai ake amfani da shi (hekta 34,000,000), kamar yadda alkaluman Babban Bankin Duniya suka nuna a 2016. Wannan bai sauya sosai ba tun 2011.

Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa kashi 77 cikin 100 ne na kasar Najeriya ake iya noma a kanta. Wato kusan kilomita 708,000.

TATTAUNA Danna ka tattauna

Tabbatar da gaskiya

Za mu yi kokari mu fitar da bayanai sahihai dangane da alkawuran da suka yi daga bayanan da muka samu.

Za mu mayar da hankali a kan abubuwan da ke damun mutanen karkara musamman wadanda manyan jam'iyyun suka bayyana.