Mutum 7 sun mutu a Fatakwal wurin taron APC

Dubban magoya bayan jam'iyyar APC a Najeriya suka halarci wannan taro a Fatakwal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban magoya bayan jam'iyyar APC a Najeriya a Fatakwal

A kalla mutum bakwai ne suka mutu a wani turmutsitsi da aka samu a wajen gangamin yakin neman zaben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Lamarin ya faru ne a wani filin wasa da ke garin Fatakwal, inda magoya bayansa suka yi ta turmutsitsi kusa da kofar shiga filin bayan da shugaban ya gabatar da bayaninsa.

Kasar dai za ta gudanar da zabe a ranar Asabar, inda Shugaba Buharin yake neman wa'adi na biyu.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar shi ne ake gani a matsayin babban abokin karawar Shugaba Buhari.

Me ya faru a wurin gangamin?

Wannan lamarin ya faru ne bayan da shugaban kasar ya gabatar da jawabinsa da misalin 3:00 na rana a filin wasa na Adokiye Amiesimaka.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da lamarin ya shafa sun fadi kasa ne, daga nan sai aka tattake su a daidai lokacin da taron jama'ar suke kokarin kutsawa ta wata kofa domin su raka Shugaba Buhari domin fita daga filin.

An kai mutanen da suka samu raunuka asibitin da ke kusa da filin taron.

Bayan faruwar wannan lamarin, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa an sanar da shugaban cewa an samu ''mutuwar magoya bayan 'yan jam'iyyar APC da dama a wani turmutsitsi.''